Abdul'ziz Yari ya bawa Shugaba Tinubu Gudumawar Kayan Abinci da Mutum Fiye da Miliyan biyu zasu Amfana
- Katsina City News
- 10 Mar, 2024
- 449
Sanata Abdulaziz Yari Ya Baiwa Shugaba Tinubu Gudummawar Kayan Abinci A Rabawa Ƴan Nijeriya Sama Da Mutane Milyan Biyu
Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar, ya ba da gudunmawar tirelolin shinkfa da ƙunshin kayayyakin masarufi waɗanda suka haɗa da shinkafa, mai, taliya, suga, makaroni, gishiri, da sauransu domin a rabawa talakawa masu ƙaramin ƙarfi su rage raɗaɗin halin tsadar rayuwa da ake ciki gami da samun abin shiga Ramadan ga waɗanda suke musulmai.
Babban mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz ne ya jagoranci waɗanda suka wakilci Shugaba Tinubu domin shaida yadda ake rabon kayayyakin abincin a wuraren ajiya dake Abuja da Kano.
Onarabul Muhammad Garba Gololo wanda ya kasance wakilin Sanata Yari wajen miƙa kayan a Abuja ya bayyana cewa sun ba wa shugaba Tinubu wannan gudunmawa ne domin su tallafawa ƙoƙarin gwamnatinsa wajen ragewa al'ummar Najeriya raɗaɗin halin da suke ciki.
"Muna sa ran za a raba wannan kaya ga gidajen ƴan Najeriya sama da mutum miliyan biyu musulmai da waɗanda ba musulmi ba a duk faɗin Najeriya," in ji shi.
Da yake jawabi a yayin duba rabon shinkafa daga rumbunan ajiya dake Kano, Dr Abubakar Nuhu Damburam, wanda ya wakilci Sanata Abdulaziz yari ya ce za a raba buhunan shinkafa dubu tamanin da hudu (84,000) ga mabuƙata ta hannun malaman addini, sarakuna da kuma sauran shugabannin al'umma.
Da yake maida jawabi, babban mai taimakawa shugaban ƙasa Tinubu kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya yabawa Sanata yari bisa wannan ƙoƙari tare da kira ga sauran masu hali da su yi koyi da shi wajen tallafawa al'umma masu ƙaramin ƙarfi kamar yadda shugaban ƙasa ke kiraye-kirayen a yi hakan.
"Wannan abun farin ciki ne da yabawa, a madadin mai girma shugaban ƙasa, muna godiya da wannan tallafi ga mabuƙata, Allah Ya saka da alkhairi. Muna fatan sauran masu hali za su yi koyi da hakan wajen tallafawa masu ƙaramin ƙarfi batare da bambancin addini, ƙabila ko siyasa ba" Cewar Malam Abdul'aziz Abdul'aziz, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Tinubu kan harkokin sadarwa.