Kadan daga Falalar Ranar Juma'a
- Katsina City News
- 01 Sep, 2023
- 1098
Juma‘a ita ce mafi girma a cikin ranaku da ALLAH Madaukakin Sarki ya halitta, ta yadda ya bawa yahudawa zabi sai suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa nasara zabi sai suka zabi lahadi, mu kuma al‘ummar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam sai ALLAH ya azurta mu da wannan rana ta juma‘a.
A cikin tane ALLAH Madaukakin Sarki ya halicci babanmu Annabi ADAM (AS) kuma a cikin wannan
rana aka sauko da shi daga AL-JANNAH, kuma a cikin irin wannan rana ALLAH Madaukakin Sarki zai
tashi alƙiyama.
Hadisi ya tabbata a cikin muslim cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace idan ranar juma‘a ta zo duk halittun ALLAH
Madaukakin Sarki hankalinsu a tashe yake (sabo da tsoran kada ALLAH ya tashi ƙiyama a wannan
ranar).
Sai mutum da al-janni
kawai hankalin su yake a kwance.
Haka kuma yana daga falalar ta juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wasallam yace akwai wata sa‘a wanda duk ya risketa yana
mai addu‘a to ALLAH zai karbi addu‘arsa.