Yadda Zagayen Duba Ayyuka Ya Gudana A Kananan Hukumomin Yankin Katsina
- Sulaiman Umar
- 02 Mar, 2024
- 555
Daga Sulaiman Umar
Tawagar gani da ido na musamman wanda mai girma gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya kafa ta ziyarci kananan hukumomin yankin Katsina domin ziyarar gani da ido na ayyukan alkhairi daban daban da kungiyar AGILE ta gudanar a fadin jihar. Kamar dai yanda ya gudana a wancan makon da ya gabata, a wannan makon ma tawagar ta samu ziyartar kananan hukumomin yankin Katsina domin duba wadannan ayyuka na AGILE da kuma wasu ayyuka na musamman tare da isar da sakon sada zumunci da fatan alkhairi ga ‘yan jam’iyya.
Tawagar wanda mai girma mukaddashin shugaban APC na jihar Katsina Alh. Bala Abu Musawa ke jagoranta tare da manyan jagororin ‘yan tawagar wanda suka hada da mai ba wa gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-gwajo, ciki harda Hon. Sabo Musa sun ziyarci duba wadannan ayyuka ne a kananan hukumomin yankin katsina 11 a wannan makon wanda suka hada da karamar hukumar Danmusa, Safana, Kurfi, Batsari, Jibia, Kankia, Rimi, Batagarawa, Charanci da karamar hukumar birnin Katsina, a inda aka gudanar da ziyarorin daki-daki tare da rakiyar shuwagabannin kananan hukumomin domin shiga kowane lungu da sako na karamar hukuma domin tabbatar da wadannan ayyuka da aka gudanar wadanda suka hada da gina makarantun sakandare da gina asibitoci da ayyukan hanya da kungiyar ta aiwatar a birnin Katsina da karkara.
A yayin ziyarar, shuwagabannin kananan hukumomin sun bayyana nasu muhimman aikace-aikacen jinkan da suka gudanar a yankunan kananan hukumomin nasu gabannin zaben kananan hukumomi da ke kusantowa a wannan shekara.
A yayin jawabin shugaban tawagar a kowace karamar hukuma Alhaji Bala Abu Musawa yayi jawabin jan hankali inda yayi nuni da irin alkhairin da kungiyar AGILE ke tafe dashi kamar yadda aka gani kuma ya gudana.
“Hukumar AGILE Muna mata fatan alkhairi bisa wannan ayyuka na jinkai da ta ke gudanarwa a Jihar Katsina, domin haryanzu mudai alkhairin ta muke gani”
“Muna wannan ziyara ne domin abubuwa guda 4, na farko shine mu gana da shuwagabannin jam’iyya mu gansu su ganmu, muyi musanyan Magana tare da yi wa juna fatan alkhairi mu kuma yi wa wannan gwamnatin ta Radda Karin godiya da Allah ya bashi sa’a ya kirkiro da wannan alawus na shuwagabannin jam’iyya, hakika wannan sabon abu ne yana isowa garemu kuma muna jin dadinshi, saboda haka idan muka godewa Allah zai kara mana, Malam Dikko Radda ya cancanci yabo da godiya.”
Shugaban tawagar Alhaji Bala Musawa ya cigaba da jan hankalin shugabannin Jam’iyya da su saka alkhairi da alkhairi da kuma tabbatar da biyayya ga jam’iyya.
“shuwagabannin jam’iyya a daure tunda dai ga Dikko Radda ya canza mana muna kuma fatan zai kara mana indai muka gode wa Allah, saboda haka a daure dunga fadin alkhairi akan jam’iyya, wannan matsin rayuwa da ake cewa tsada munsani mu musulmai ne ba kuma mai iya canza shi sai ubangiji, ubangijin da yayi mu shike da zamani yake kuma juya shi yadda ya so, ba wai tsadar al’amuran bane a’a kaidai Allah ya hore ma abin yi.”