MINISTAN AYYUKA YA JINJINA MA GWAMNAN ZAMFARA
- Katsina City News
- 01 Mar, 2024
- 685
@ Katsina Times
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samu yabo daga Ministan Ayyuka, David Umahi, bisa gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu a ayyukan sabunta birane.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ministan ya kai ziyarar aiki Jihar Zamfara a wani rangaɗin da yake yi na duba ayyukan titunan Gwamnatin Tarayya a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce ministan ya duba ayyukan titunan Gwamnatin Tarayya da ke gudana wanda ya kai tsawon kilomita 277.305, daga Zariya zuwa Sheme, Sheme zuwa Gusau, da Gusau zuwa Mafara.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ministan da muƙarrabansa sun lura da ɗumbin nasarorin da aka samu a aikin sabunta biranen da gwamnatin Gwamna Lawal ke gudanarwa.
A nasa jawabin, gwamna Lawal ya yaba wa ministan bisa yunƙurinsa na duba ayyukan manyan titunan Gwamnatin Tarayya.
“Ina tabbatar muku da cewa akwai alheri domin akan bayar da kwangilar gina tituna, amma babu wanda ke zuwa dubawa daga Gwamnatin Tarayya. Zuwar ku na da matuƙar amfani..
“Minista, kamar yadda ka tabbatar, ba a daina faɗaɗa hanyoyi ba, kamar yadda ake ta yayatawa. Wannan labari ne mai daɗi.
“Ina so in nuna godiyata da kyawawan kalamanka. A matsayinmu na gwamnati mai kishin ƙasa, muna aiki tuƙuru don ganin mun canja mummunan yanayin Jihar Zamfara. A da, duk lokacin da ka ji labarin Jihar Zamfara, a kan yi tunanin abu mara kyau ne. Amma yanzu muna ƙoƙarin ceto da sake gina jihar.
“Ina kuma son in yi godiya ga shugaban ƙasa bisa ga ƙoƙarin da ya yi na aiwatar da muhimman ayyukan Gwamnatin Tarayya. Za mu ci gaba da goyon bayan kyawawan manufofinsa.”
A yayin jawabinsa, ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne umarci a yi rangaɗin domin ganin yadda ayyukan ke gudana.
“Gwamna, mun zo nan ne bisa umarnin shugaban ƙasa domin duba ayyukan tituna da ke gudana tare da isar da gaisuwarsa gare ku.
“Shugaban ƙasa ya ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa, da suka haɗa da faɗaɗa titunan tarayya, ba a Zamfara kaɗai ba har ma a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.
"Ina yaba muku kan ƙoƙorin ku na ci gaba da aiwatar da ayyukan sabunta birane da suka kawo sauyi a Zamfara cikin watanni tara kacal."
Shugaban kwamitin Majalisar Dattijai mai kula da gidaje da tituna, Aminu Waziri Tambuwal, tsohon gwamnan Jihar Sakkwato yana cikin tawagar ministan.