Jam'iyyar APC a jihar Katsina ta yabawa shugaban Karamar hukumar Kaita
- Katsina City News
- 01 Mar, 2024
- 626
Uwar Jam'iyyar Apc ta Jihar Katsina ta yaba ma shugaban karamar hukumar Kaita, akan kokarin shi na samar da ayyukan raya kasa da taimakon Al'umma.
Mataimakin shugaban Jam'iyyar Apc na Jihar Katsina, Alhaji Bala Abubakar Musawa ya yi wannan yabon amadadin uwar Jam'iyyar.
Yayin ran gadin duba ayyuka da uwar Jam'iyyar keyi a fadin jihar wanda kananan hukumomi da Jiha su ka gudanar karkashin Gwamnatin Dr. Malam Dikko Umar Radda.
Mataimakin shugaban Jam'iyyar yace" sun gamsu da irin ayyukan raya kasa da shugaban karamar hukumar Kaita Hon. Engr. Bello Lawal Yandaki ya gudanar a cikin karamar hukumar.
Haka zalika Jam'iyyar ta gamsu akan yadda shugaban karamar hukumar yake rike da 'yan Jam'iyya da 'yan siyasa da kuma taimakon sauran Al'umma gaba daya bakin gwalgwadon hali.
Alhaji Bala Abu Musawa ya yaba ma shugaban karamar hukumar Kaita sosai musamman kasuwa da ya gani da idonsa ya gina sukutum da shaguna a cikin garin Yandaki da hanyoyin ruwa, a cikin garin Gafia da sauran ayyukan da ya yi, a cikin karamar hukumar na raya kasa.
Bangaren kula da 'yan siyasa da Jam'iyya da sauransu, Alhaji Bala Abu ya yaba ma shi akan yadda yaga takarda rubuce na yawan mutanen da ya taimaka ya basu kwangiloli, domin ci gaba da raya Jam'iyya, a cikin karamar hukumar Kaita.