JAHAR ZAMFARA ZATA HADA GWAIWA DA KASAR SWEDEN.
- Katsina City News
- 18 Feb, 2024
- 601
Katsina Times
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bay yana cewa a shirye ya ke ya haɗa hannu da ƙasar Sweden a fannoni da dama, waɗanda suka haɗa da ilimi, Harkar lafiya da samar da makamashi.
Gwamna Lawal ya furta haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ambasadar ƙasar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund cikin makon da ya gabata a ofishin sa da ke Abuja, inda ziyarar ta bayar da dama wajen tattauna muhimman batutuwa.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Gwamnan ya riga ya fitar da matakan jawo masu zuba jari da tallafi daga ƙasashen waje.
Sanarwar ta Idris ta ce, “A makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin Ambasar ƙasar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund a ofishin sa da ke Abuja.
“A tattaunawar ta su, sun tattauna batutuwa da niyyar samar da haɗin gwiwa a muhimman fannoni na tattalin arziki, ƙulla kyakkyawar dangantaka da samar da manyan ayyuka don amfanin jihar Zamfara da Zamfarawa.
“Gwamna Lawal ya kuma ƙara tabbatar wa da baƙuwar tasa cewa a shirye gwamnatin sa ta ke wajen haɗa hannu da Sweden don samar da ci gaba a fannoni da dama.
“Ƙasar Sweden ta nuna buƙatun ta na haɗa hannu da jihar Zamfara na samar da dangantaka mai ɗorewa, tare da aiwatar da ayyukan ci gaba don amfanin al'ummar jihar a Nijeriya."
Bugu ta ƙari, Ambasadar ta yi alƙawarin samar wa Zamfara masana a harkar haƙan ma'adinan ƙasa, dabarun noma na zamani, tallafawa don inganta ilimi, harkokin kiwon lafiya da samar da hasken wutar lantarki na Sola.