NAHCON ta Sanar da Kudin Hajjin Bana Duk da Hauhawar Dala.
- Katsina City News
- 03 Feb, 2024
- 449
Duk yadda Shugaban Hukumar Aikin Hajjin ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi yaso kudin Hajjin Bana kada ya haura abunda Maniyyata suka ajjiye na naira miliyan hudu da rabi, farashin dala ya hana hakan ya kasance.
Shugaba Jalal Ahmad Arabi yayi iya yinsa don masu bada hidimomi ga Alhazai su karyar da farashinsu, hakanne yasa aka samu saukin da badan shi ba da sai farashin kujerar bana ya zama sama da miliyan shidda. Da yardar Allah sai kudin Hajjin Bana ya zama kamar yadda za a gani anan kasa:
Maniyyata daga Kudancin Najeriya za su biya: Naira miliyan hudu da dubu dari takwas da casa’in da tara wato (N4,899,000); Maniyyatan Arewa kuwa za su bada Naira miliyan hudu da dubu dari shidda da casa’in da tara wato (N4,699,000); Amma Maniyyata daga Jihohin Borno da Adamawa kuwa za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da saba’in da tara watau (N4,679,000) don zuwa sauke Faralin shekarar dubu biyu da ashirin da hudu (2024).
Shugaban NAHCON na la’akari ne da wa’adin da Saudi Arebiya ta gindaya ne na ashirin da biyar ga watan da muke ciki na Febrairun Shekaran nan ya zama ranar da za’a rufe biyan kudaden.
Saboda haka ya zama dole Maniyyata su gama cikasa kudinsu kafin ko kuma kada ya gota ranar Litinin sha biyu ga watannan na fabrairu don NAHCON ta iya aike kudaden zuwa Saudiyya kafin cikar wa’adin da ta gindaya.
NAHCON na da azamar ganin an samu cikakkiyar nasarar gudanar da Hajjin Bana duk da kalubalen da ake dasu da kuma jinjinawa Musulman Najeriya saboda hadin kan da suka bayar cikin wannan yanayi na rashin-tabbas da ake ciki.
Fatima Sanda Usara,
Mataimakiyar Darakta
Sashen Hulda da Jama’a,
NAHCON
Fassarar Muhammad Ahmad Musa