Dan Majalisar Wakilan Nijeriya daga Kananan Hukumomin Kankara, Faskari, Sabuwa ya raba Kayan Jinƙai a Yankin
- Katsina City News
- 25 Jan, 2024
- 517
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Honorabul Muhammad Jamilu (Lion) Danmajalisa mai Wakiltar Kananan Hukumomin Kankara, Faskari da Sabuwa a jihar Katsina ya raba kayan Jinkai da Motocin Ɗaukar Marasa Lafiya a yankunan
Honorabul Lion da ke rike da mukamin Mataimakin Shugaban Kwamitin Sashin Dumamar Yanayi wato (Climate Change) a majalisar ta Tarayya ya raba kayan abinci buhunnan Shinkafa da Dangogin su domin Marasa karfi a yankunan Kananan Hukumomin uku.
Haka zalika Honorabul Lion Magayakin Faskari ya bada Umarnin gyaran Dukkanin Famfunan Tuƙa-tuƙa dake Mazabun Garagi wato (Garagi Ward) a karamar hukumar Ƙanƙara.
Motar Daukar Marasa Lafiya Kirar (Gulf) ga Al'ummarsa ta Garagi don rage dawainiya zuwa Babbar Asibitin Kankara. Haka kuma Magayakin Faskari ya bada Babbar Mota Ambulance da Dukkanin Kayayyakin Aikin ta a Babbar Asibitin Kankara domin saukaka wa Fannin Lafiya.
Shinkafa da sauran kayan Abinci da Al'ummar suka amfana da su, sun nuna jin dadin su ga Honorabul Muhammad Jamilu Lion akan wannan Kulawa da suka bayyana cewa basu taba samun Danmajalisar da ya kula ya kuma damu da kukansu kamar sa ba.
Da yake gabatar da Jawabin sa a wajen Taron Magayakin Faskari Honorabul Muhammad Jamilu Katsina ya nuna jin dadin sa irin yanda yaga al'umma na nuna masa soyayya da goyon baya, Lion ya sha alwashin yin iya kokarinsa na ganin al'ummar yankin sun samu tallafi duk irin wanda ya taso ba tare da nuku-nuku ko karkatarwa kamar yanda wasu ke yi ba.
Yace da yardar Allah sai dan yankin Kankara Faskari da Sabuwa dama Jihar Katsina sun samu dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A karshe ya nemi goyon bayan al'ummar da basu hadinkai domin Inganta Rayuwarsu ta hanyoyi daban-daban.
Taron da aka gudanar a karamar hukumar Kankara ranar Alhamis ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a yankunan na kananan hukumomi uku da Dattawa da sauran al'umma magoya bayan Jam'iyyar PDP.