ƁARAYIN DAJI SUNKAI MA JAMI'AN TSARO HARIN KWANTON ƁAUNA A BATSARI
- Katsina City News
- 19 Jan, 2024
- 711
Misbahu Ahmad @Katsina Times
Ɓarayin daji masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, sunkai ma jami'an tsaro hari a ƙauyen Sakijiki (Bakin gulbi) dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru a ranar alhamis da misalin 08:00pm na dare, inda suka saɗaɗa suka afka ma jami'an tsaron ƴan sandan kwantar da tarzoma dake aiki bada tsaro a ƙauyen.
Maharan sun shammaci jami'an tsaron domin sun fito masu ta inda basu zata ba kuma ba tare da wata masaniya ba daga mutanen yankin.
Wani mazaunin garin ya bayyana mana cewa ɓarayin sun kashe jami'in tsaron Dan sanda ɗaya san nan sun jikkata Dan sanda ɗaya wanda tuni aka garzaya da shi asibiti domin ceto rayuwarshi, sannan sun sace bindigunsu.
Mun kokarin jin ta bakin jami in hudda da jama a na yan sanda amma bamu same shi a waya ba.mun aika masa sakon rubutu ba amsa.
Sai dai wani jimi in soja da bai son a bayyana sunan sa ya tabbatar mana da labarin. Yace sun fafata da barayin kafin su kora su.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762