BARAYIN DAJI SUN KAIMA SANSANIN SOJA HARI A BATSARI
- Katsina City News
- 15 Jan, 2024
- 737
Misbahu Ahmada @Katsina Times
Gungun Barayin daji dauke da muggan makamai sun kai Hari garin Nahuta dake karamar hukumar Batsari jahar Katsina.
Wani dan garin ya shaida ma jaridun Katsina Times cewa barayin sun fara kai Hari sansanin sojoji dake garin.
Soja sun mayar masu da wuta sosai, amma barayin sun fisu yawa sun kuma shammace su,don haka dole sojojin suka janye.Barayin sukayi nasarar shiga sansanin suka banka ma wasu motoci da kayayayyaki wuta.
Ganau ya tabbatar ma da jaridun Katsina Times cewa dakewar da sojojin sukayi da sun samu taimakon jiragen yaki na sama da sun ci galabar barayin.
Barayin sun kuma shiga garin na Nahuta inda suka balle shaguna da shiga gidajen mutane suka tafi da kayayyakin da dabbobi.
Zamu zo da cikakken Rahoton nan gaba kadan
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 080577777762