Hukumar Hizbah ta sha alwashin kawo karshen Barace-barace a jihar Katsina
- Katsina City News
- 28 Dec, 2023
- 539
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A zantawar sa da Katsina Times, shugaban hukumar ta Hizbah a jihar Katsina Dakta Aminu Usman (Abu Ammar) ya bayyana cewa, sam! bara ba Addini bace, hasali ma tana jawowa Addinin Musulunci Kaskanci.
Yace babu wani Sahabi, a zamanin Annabi (S) da yaje yana bara, don haka babu dalili kai Musulmi musamman ka buge da bara, kuma abin kaskanci har a Coci.
Kwamandan na Hizbah ya bayyana cewa, "Gwamnatin jihar Katsina ta samar da tsari da zai yi maganin wannan matsala, "An Kafa Hizbah da zamu fita rangadi mu shiga lungu da sako ba a Coci ba har a masallatai don zakulo mabaratan nan, mu tantance su, mu gane masu bukatar taimako da gaske mu damkawa hukumar Zakka da Waqafi, da Gwamna Radda ya samar don basu gudumawar da ta dace."
Dakta Aminu Usman ya ja hankalin Iyayen Yara da sauran masu aikata wasu laifuka na ba daidai ba a jihar Katsina da su shiga taitayinsu, yace, "ba zamu zura ido Matasan mu da su ne goben mu ba suna shaye shaye." Yace "babu wani mutum da yake so dansa ya lalace, don haka muke neman Iyaye su sanyawa 'ya'yan su ido, kuma su bamu hadin kai domin samar da gobe mai kyau."
Shugaban na Hizbah ya yi kira ga Al'ummar Musulmi a jihar Katsina da Manyan Malamai cewa su zo a hada kai da fahimtar juna don Aiki tare, sabida hukumar Hizbah ba ta 'yan Izala bace, hukumar Hizbah ta Al'ummar Katsina ce kuma Al'umma zata yiwa Aiki, yace don haka za'aga Dan'izala, dan Shi'a dan ɗariƙa da dan Al'quraniyun a ciki, yace hatta Kiristoci na jihar Katsina zasu zauna dasu su samu fahimtar juna don suma suna son al'ummar su su zama mutanen kirki.
Dakta Aminu ya bayyana cewa zasu ziyarci dukkanin bangaren malaman Addini a hukumance don a gudu tare a tsira tare.
A karshe ya yabawa Gwamna Malam Dikko Umar Radda akan yanda ya bawa hukumar dukkanin goyon baya da hadin kai don ganin al'ummar jihar Katsina sun samu kyakkyawan yanayi ta ko wace fuska.