Tarihin Garin Jibiya

top-news

JIBIYA 

  Garin Jibiya na can Arewacin Birnin Katsina kimanin kilomita 42. Garin Jibiya yayi iyaka da  Jamhuriyar Nijar da Kuma Jihar Zamfarar Najeriya. 

   Garin Jibiya kamar yadda Tarihi ya nuna  bai wuce shekaru Dari da wani abu da kafuwa ba. ( Kagara 1951) ya bayyana cewa Sarkin Katsina Muhammadu Dikko(1906-1944) Yana da babban tasiri wajen Kafuwar Garin Jibiya. Ance  adai dai shekarar 1906 Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya sari Garin Jibiya, domin duk arewacin Kasar Katsina a wannan lokaci babu wani Gari Mai girma Wanda idan Sarki ya fito rangadi ko farauta zai tsaya ya huta. Wannan dalili ne yasa Sarkin ya sari Jibiya. A lokacin Mulkin Dallazawa, Garin Zandam da Bugaje da suke a karkashin Jibiya yanzu, sun taba zama hedikwatar mulki ta Hakimi, a karkashin Sarkin Sullubawa, Wanda Ummarun  Dunyawa ya farayi bayan kare Jihadi a shekarar 1807, Wanda ya Fara zama a Zandam  daga baya acikin  shekarar 1828 ya maido hedikwatar shi Bugaje saboda rikicin yakin Katsina da Maradi, wannan ya nuna Zandam da Bugaje sun riga Garin Jibiya kafuwa. 

     Ta fannin Sarauta kuma, mutum na farko daya Fara Sarautar Jibiya shine Gatari Duma acikin shekarar 1909.  Bayan rasuwar Gatari Duma, Sai aka nada dansa Gatari Ibrahim Acikin shekarar 1926. A lokacin sane aka dauke Kasuwar Jibiya daga  cikin gari aka maida  da can Yammacin Garin inda take yanzu. Haka Kuma alokacinsa ne aka bude Dakin Shan magani na farko. 

  Da tsufa ya Kama Gatari Ibrahim Sai yayi murabus a shekarar 1957 aka nada dansa Alhaji Rabiu Ibrahim amma da sunan Hakimin Jibiya, Sarkin Arewan Katsina. Bayan rasuwarsa Sai aka nada dansa  Mai suna Alhaji Rabe Rabi'u Ibrahim. To har yanzu shi ke Sarautar wannan Gari. 

   Dama dai Kasar Jibiya na da fadamu da dausayi domin Kasar Zandam da Bugaje duk   cikin Kasar Jibiya suke a halin yanzu. Su Kuma wadannan garuruwan tun  da dadewa mutanen su su kware wajen noman Rani da kiwo, saboda samun dausayi Mai kyau. 

 . Hakanan Kuma mutanen Jibiya  Yan Kasuwane na gaske, saboda kasancewarsu kan iyaka da Jamhuriyar Nijar. Kasuwar Jibiya na daya daga manyan  kasuwannin mako na  Kasar Katsina. Mutane daga ciki da wajen Kasar nan na zuwa cin Kasuwar a ranar Lahadi, mutanen garuruwa kamar Zariya, Sokoto, Kano, Katsina  da Kuma Makwabta na Jamhiriyar Nijar duk suna zuwa wannan Kasuwa. 

   Ta fannin ilimi Garin Jibiya ya samu makarantar Boko tun 1936 sannan an bude makarantar Boko ta jeka ka dawo  a shekarar 1983, tare da Kuma makarantar Yanmata ta kwana dai dai wanna shekarar. Ta fannin makarantun addinin Musulunci akwai makarantun Allo da Islamiyya da dama a Garin Jibiya. Akwai fitattun malaman addinin Musulunci a Garin Jibiya irinsu Malam Kore dan Madarunfa, Malam Lawal Makaho, Malam Musa Takamslamai da sauransu. 

   Garin Jibiya ya Kara bunkasa alokacin da ya zamo Hedkwatar Karamar hukumar Jibiya wadda aka kirkiro a shekarar 1989.   Wannan Sabon matsayi da Jibiya ta samu ya kawo Mata Karin abubuwan more rayuwa kamar hanyoyin cikin Gari  wadanda aka zubawa kwalta da  hada Garin Jibiya da wutar Lantarki wadda akayi bukin budeta a shekarar 1998, wadda tsohon shugaban Kasa na Soja Janar Abdulsalam yayi tare da bude Kasuwar  kan iyaka wadda aka  Gina Jibiya duk a cikin wannan lokacin. 

   Ta fannin noman Rani Jibiya ta samu katafaren Dam din nan Wanda aka Fara gininsa tun  1987, shugaban Kasa na Soja Janar Ibrahim Babangida yayi bikin bude say shekarar 1991. Kuma gwamnan Soja na Katsina Chama ya  gina wani dandalin furanin kallo domin Yan yawon Shakatawa da bude ido. Ana Kiran wurin Chama Park. 

    Ta fannin siyasa mutanen Jibiya ba a bar su a baya ba domin kuwa suna taka rawa sosai a duk lokacin da siyasa ta kunno Kai. Suna da fitattun Yan Siyasa irinsu Honourable Sada Soli Jibia, Honourable Aminu Lawal Jibia, Honourable Yusuf Sule, Honourable Salusu Salisco da sauransu. 

  Soures. 

1. Garuruwan Jihar Katsina na III, na Hukumar binciken Tarihi da kyautata al'adu ta Jihar Katsina. 

2.  Kagara (1951) Walin Katsina. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko(1865). 

Alhaji Musa Gambo Kofar soro.

NNPC Advert