ME AKE CIKI DA KANSILOLIN KARAMAR HUKUMAR SAFANA? ...Suna kan mukamansu ko an canza su?
- Katsina City News
- 25 Dec, 2023
- 571
Suleiman Umar @ Katsina Times
A kakar yakin neman zaben shekarar 2023. Dan majalisar tarayya mai wakiltar safana, Dan Musa da Batsari, Alhaji Ahmad Dayyabu ya shelanta komawa, jam iyyar PDP ya kuma canza sheka da mutanen shi masu yawan gaske, cikinsu har da kansilolin karamar hukumar safana guda biyar da wasu masu rike da mukamai a jam iyyar APC na kananan hukumomin safana,Dan Musa,da Batsari.
Bayan kammala zaben shekarar 2023 da ratsar da sabbin yan takarar da aka zaba.siyasar kuma sai ta chanza, inda Alhaji Ahmad Dayyabu. Wanda bai yi takara ba a zaben na shekarar 2023, ya sake dawo jam iyyar ta APC tare da mutanen sa baki daya.ciki har da kansilolin da suka chanza sheka daga jam iyyar APC zuwa PDP.
A karamar hukumar safana, sunyi amfani da wata dokar data ce idan ka chanza jam iyyar da ta kawo Wanda aka zaba mulki to ya rabu da mukaminshi,suka Dakatar da albashin kansilolin hudu da suka rubuta takardar chanza sheka .
Kansilolin sune na mazabun Baure B.Tsaskiya,zakka da Babban duhu B. Duk da tsaida masu albashi,kansilolin sunci gaba da zuwa Ofis ba tare da an hana su ba.amma ba albashi ba kuma abin da akeyi dasu.
Yanzu wata Goma sha daya da faruwar lamarin,ana neman a nada masu kansilolin riko duk da sun dawo jam iyyar ta APC.wanda ba ayi haka ba, a can baya.
A ranar litinin 18 ga watan Disamba 2023.shugaban Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam iyyar APC a karamar hukumar safana, Alhaji Abduljalal liliya Runka ya Kira ya Kira taron na masu ruwa da tsaki na jam iyyar inda ya bayyana ma mahalarta taron cewa, an chanza sunayen kansilolin da suka chanza sheka zuwa wata jam iyya.ya bayyana sunayen wadanda za a nada a matsayin kansilolin riko kafin zabe.
Wasu mutane wadanda suka fito daga yankin da kansilolin da za chanza suke, sun bayyana ma jaridun Katsina Times cewa su suna bukatar kansilolin da suka zaba.kuma zasuyi fatan tun da sun gane kurensu sun dawo jam iyyar ta APC ayi hakuri a kyale su.
Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na jam iyyar ta APC Wanda bai son a bayyana sunan shi, yace hakuri da kyale kansilolin shine zai kawo dai dai to, a siyasar ta safana.
Yace kansiloli ne, da bangarorin siyasa na safana suka kawo su.idan aka taba su anyi ma wani bangaren gibi kuma zai iya kawo baraka da zaman lafiyar jam iyyar.
Ya kara da cewa, siyasa yar a bata ne, kuma a shirya don haka a shirya kawai a tarbi gaba.
Kashi 80 cikin dari na wadanda jaridun Katsina Times tayi magana dasu a yankin da kansilolin suka fito, suna goyon bayan a kyale wadanda aka zaba su kammala wa adinsu.kar a nada masu wasu kansilolin riko.
A zantawar da mukayi da Honourable Abduljalal liliya Runka ta waya,cewa yayi doka ce ta kori wadannan kansilolin saboda sun bar jam iyyarsu.
Ya kuma ce, sun canza su ne, da kansilolin riko wadanda zasu rantsar da ciyaman din karamar hukumar ya sanya lokaci bisa tanadin doka.
Lokacin da muka tuntubi shugaban karamar hukumar ta Safana ta waya,cewa yayi bai San da ranar rantsar da sabbin kansilolin ba,a yanzu babu wannan maganar a gaban shi.
Shi kuma Alhaji Bala Abu Musawa cewa yayi matsalar kansilolin safana matsala ce, mai yar karamar sarkakkiya, amma a siyasa babu abin da zai gagara warwarewa kuma suna tattaunawa da neman mafitar da za tayi ma kowa dai dai ba kuma tare da an bata ma kowa ba.ya kara da cewa siyasa ta gaji hawa da sauka kuma ba abin da ke gagara a siyasa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762