Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ta Amince Da jimlar N454,308,862,113.96 a Matsayin Kasafin Kudin Shekarar 2024
- Katsina City News
- 18 Dec, 2023
- 746
Yanzu-Yanzu: Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ta Amince Da jimlar N454,308,862,113.96 a Matsayin Kasafin Kudin Shekarar 2024
Hakan ya biyo bayan amince wa da rahoton da kwamitin Majalisa mai kula da kasafin kudi ya gabatar a karkashi jagorancin Hon. Lawal H. Yaro.
Bayan an yi karatu na uku akan tayin dokar, sai Shugaban Majalisar Dokokin Rt.Hon Nasir Yahaya ya umurci akawun Majalisa daya fitar da kwafin dokar da aka amince domin mika wa maigirma Gwamnan Jihar Katsina ya rattaba mata hannu.
Da fatan Allah ya sa albarkar sa a cikin kasafin kudin shekarar 2024 a Jihar katsina
Aminu Magaji Idris
CPS KTHA