Mai martaba Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim (Kirmau Mai Gabas) ya nuna alhininsa na rashin da aka yi a Tudun Biri da ke jihar Kaduna wanda jami'an sojojin ƙasar nan suka aiwatar bisa kuskure.
- Sulaiman Umar
- 11 Dec, 2023
- 588
Mai martaba Sarkin na Gaya Ya yi addu'a ga wadanda suka rasa rayukansu Allah ya jiƙan waɗanda aka rasa Allah ya karɓi shahadar su. Sannan marassa lafiya Kuma Allah ya ba su lafiya ya sa kaffara, Amin. Sarkin ya yi kira ga Fadar Sarkin Musulmi Sultan Abubakar Sa'ad na uku da a tabbatar an yi adalci ga wanda wannan iftalain ya faɗo musu a kuma hukunta wanda suke da hannu. Daga nan ya nemi ga Jami'an Ƙasar nan da su dinga nuna ƙwarewa a ayyukan su dan kauce wa duk wani abun ƙi da za su zamo abun zargi a nan gaba, amin.