Wane irin ciwon ciki ne yake turnuƙe sojojin Isra'ila da suka je yaƙi Gaza?
- Katsina City News
- 10 Dec, 2023
- 583
Ƙwayar cutar bakteriya ta shigella na bazuwa ne ta hanyar taɓa dagwalon bayan gida
9 Disamba 2023
Likitoci sun ce wasu a cikin dakarun sojin Isra'ila da ke faɗa a mamaye ta ƙasa a Gaza, suna fama da wani matsanancin ciwon ciki sanadin wata cuta da ake kira "shigella".
Ana jin cutar na bazuwa ne sakamakon rashin yanayi mai tsafta da kuma abinci maras aminci a fagen yaƙi.
Yaya ciwon cikin shigella ke bazuwa tsakanin dakarun Isra'ila?
Likitoci da yawa a Rundunar Sojin Isra'ila sun ba da rahoton ɓullar matsananciyar cutar ciwon ciki tsakanin dakarun da ke Gaza, a cewar Dr Tal Brosh, daraktan Sashen Cutuka masu Yaɗuwa a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Assuta Ashdod.
Ya ce ya gano suna fama da cutar da ake kira shigella ne.
Sojojin Isra'ila mai yiwuwa sun kamu da cutar shigella ne daga abincin da dangi da abokan arziƙi ke aika musu
Ana keɓe sojojin da suka kamu, sannan a mayar da su gida don yi musu magani.
Dr Broch ya ce "fayyataccen sanadi" guda da ya janyo ɓarkewar cutar shi ne abincin da fararen hula 'yan Isra'ila suka girka kuma aka aikawa dakaru a Gaza.
Ya ce mai yiwuwa ne abincin ya gurɓata da ƙwayar cutar shigella, da sauran miyagun ƙwayoyin bakteriya, saboda rashin sanyaya abincin a lokacin da ake tafiya da shi ko kuma rashin ɗumamawa sosai kafin a ci.
canza ƙunzugun jariri mai cutar shigella
ɗosanar bayan gida a lokacin jima'i da mai fama da cutar shigella
An fi samun cutar shigella a jikin mutanen da ke gararamba babu muhalli da matafiya ƙasashen duniya da maza masu jima'i da maza da mutanen da ke da raunin garkuwar jiki.
A ina cutar ta fi zama ruwan dare a duniya?
Cibiyar Daƙile Cutuka masu Yaɗuwa ta Amurka ta ƙiyasin cewa ana samun mutane tsakanin miliyan 80 zuwa miliyan 165 da ke kamuwa da cutar duk shekara a faɗin duniya, inda take haddasa mutuwar mutum 600,000.
A 2022, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ana samun kashi 99% na masu fama da cutar shigella a cikin ƙasashe masu ƙaranci da matsakaicin samun kuɗin shiga.
Mafi yawan mace-macen sanadin turnuƙewar ciwon cikin shigella, na faruwa ne a ƙasashen Kudu da Hamadar Sahara da Kudancin Asiya, kuma kimanin kashi 60 ƙananan yara ne 'yan ƙasa da shekara biyar.
Shigella musamman ta fi zama ruwan dare a ƙasashen Kudu da Hamadar Sahara da na Kudancin Asiya
Wani nazari da masana kimiyya suka gudanar a Cibiyar Harkokin Riga-Kafi ta Duniya a Koriya ta Kudu ya nuna cewa ciwon cikin da ke haddasa kashin jini na shigellosis ya fi zama ruwan dare fiye da ninki ɗari a ƙasashen Asiya.
Kamar su Bangladesh da China da Pakistan da Indonesia da Vietnam da Thailand a kan ƙasashe masu ci gaba masana'antu.
Yaya ake maganin shigella, ko kuma kare kai daga kamuwa da ita?
Cibiyar Daƙile Cutuka masu Yaɗuwa ta Amurka ta ce ana iya riga-kafin cutar shigella ta hanyar wanke hannu a kai-a kai, ga misali:
kafin girki ko kuma cin abinci
bayan an shiga banɗaki ko kuma canza ƙunzugu
kafin wata hulɗa ta jima'i
Da yawan waɗanda suka kamu da cutar, na iya warkewa ta Shigella musamman ta fi zama ruwan dare a ƙasashen Kudu da Hamadar Sahara da na Kudancin Asiya
Wani nazari da masana kimiyya suka gudanar a Cibiyar Harkokin Riga-Kafi ta Duniya a Koriya ta Kudu ya nuna cewa ciwon cikin da ke haddasa kashin jini na shigellosis ya fi zama ruwan dare fiye da ninki ɗari a ƙasashen Asiya.
Kamar su Bangladesh da China da Pakistan da Indonesia da Vietnam da Thailand a kan ƙasashe masu ci gaba masana'antu.
Yaya ake maganin shigella, ko kuma kare kai daga kamuwa da ita?
Cibiyar Daƙile Cutuka masu Yaɗuwa ta Amurka ta ce ana iya riga-kafin cutar shigella ta hanyar wanke hannu a kai-a kai, ga misali:
kafin girki ko kuma cin abinci
bayan an shiga banɗaki ko kuma canza ƙunzugu
kafin wata hulɗa ta jima'i
Da yawan waɗanda suka kamu da cutar, na iya warkewa ta hanyar shan wadataccen ruwa da kuma hutawa.
Magugunan kashe ƙwayoyin cuta nau'i biyar suna da tasiri wajen kashe cutar shigella.
shan wadataccen ruwa da kuma hutawa.
Magugunan kashe ƙwayoyin cuta nau'i biyar suna da tasiri wajen kashe cutar shigella.