Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Kwamitin Binciken Anchor Borrower A Katsina

top-news


 A jiya ne Gwamna Dikko Umaru Radda ya kaddamar da kwamitin da zai binciki yadda aka aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na Anchor Borrower Programme a jihar.

 Kwamitin mai mutum 12 da sakataren gwamnatin jihar Katsina Alh.  Abdullahi Garba Faskari, a matsayin shugaba da sakatare Malam  Aliyu Isah, daga ofishin gwamna.

 Radda ya bukaci mambobin kwamitin da su tabbatar da amincewar da aka yi musu, ta hanyar yin aikin da aka ba su da gaskiya.

 Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnatin Katsina Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ya nuna cewa ana sa ran kwamitin zai mika rahotonsa cikin makonni biyu.

 “Daga cikin sharuddan da aka baiwa kwamitin akwai bincike kan yadda jihar ke da hannu a cikin shirin anchor Borrower Programme, da kuma tantance matakin da gwamnatin jihar ta dauka a cikin shirin.

 “Kwamitin kuma zai zakulo wadanda suka ci gajiyar shirin da kuma ko sun biya bashin da aka basu, da kuma tantance masu bin shirin, sannan kuma ya bayar da shawarwarin da za su taimaka wa gwamnati wajen magance kalubalen da ke kawo cikas.

NNPC Advert