"Bai kamata Shugaban Ƙasa ya zama Ministan Manfetur ba." -Sanusi Lamiɗo Sanusi
- Katsina City News
- 07 Dec, 2023
- 603
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a taron shugabannin bankuna da aka gudanar a dakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja.
Tsohon Sarkin Kano ya kuma yi kira da a binciki kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) inda ya ce wannan kiran ne ya sa shi ya rasa aikinsa a matsayin Gwamnan CBN.
Ya kara da cewa shugaba Tinubu bayan hawansa mulki ya raba ma’aikatar albarkatun man fetur tare da nada Ekperipe Ekpo a matsayin karamin ministan albarkatun iskar gas; da Heineken Lokpobiri a matsayin karamin minista, albarkatun man fetur amma ya ci gaba da rike mukamin babban ministan albarkatun man fetur ga kansa.
Wannan ya biyo bayan salon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne wanda kuma ya zama ministan man fetur a zamaninsa.
Amma Sanusi ya bayyana a yayin jawabinsa cewa bai kamata shugaban kasa ya zama ministan man fetur ba.
Da yake karin haske a yayin taron, tsohon Gwamnan na CBN ya kuma jaddada bukatar yin gyara ga dokar CBN domin kiyaye babban bankin daga tasirin siyasa.