Dikko Radda Ya Sake Hura Wa Kananan Hukumomi Rai
- Katsina City News
- 06 Dec, 2023
- 596
Daga Mannir Shehu Wurma PhD
Kamar yadda yake a rubuce a kundin tsarin mulkin kasar nan, kananan hukumomi wani muhimmin bangare ne mai matukar matsayi da mahimmanci a fagen siyasa da tafiyar da mulkin jama’a.
Matsayin da suke da shi na falle na uku a matakin gwamnati ya samo asali ne daga gyare-gyare fuska daban-daban da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan, tun daga rahoton Dasuki, har zuwa zamanin Babangida da aka cimma matsaya a tarukan gyaran tsarin mulki da dama da aka yi a baya.
A dunkule za a iya cewa kananan hukumomi sun zama kashin bayan gudanar da tsarin dimokradiyya a cikin al’umma daban-daban kamar Nijeriya.
Duk wani shugaban da ya damu da jin dadin jama’a ba zai iya yin watsi da wannan muhimmin bangare da ke da alaka da jin dadin jama’a ba kai tsaye.
A wani mataki na nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar talaka, Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, tun da aka kafa gwamnatinsa, ya himmatu wajen aiwatar da sauye-sauye masu ma'ana a kananan hukumomin Katsina. Wannan hubbasan da ya yi ya haifar da da mai ido ta hanyar gaskiya, rikon amana, da kuma sahihanci shugabanci a cikin ayyukan yau da kullum da ake gudanarwa a kananan hukumomi.
Wani abin mamaki shi ne, wannan shiri na gaskiya da rashin son zuciya ya haifar da muhimman sauye-sauye cikin sauri a tsakanin masu tafiyar da jagorancin kananan hukumomin jihar Katsina.
Tabbas! Lokaci ya wuce da ake hana kananan hukumomi kudadensu don su gudanar da ayyukan ci gaba. A halin yanzu, ba kawai suna samun kudade take yanke ba ne, har ma an bai wa shugabannin kananan hukumomi ’yanci da damar gudanar da ayyukan ci gaba a yankunansu ba tare da wani kaidi ba.
Wannan ingantaccen sauyi ba tunani ne kawai ba, kananan hukumomi a Katsina a yanzu sun zama cibiyoyin ayyukan mutane ci gaban mutane, an sakar masu mara suna numfasawa.
Wannan ya bambanta da lokutan baya, lokacin da sakatariyar karamar hukumar ta kasance kango, suka zama wajen da jami’an tsaro ne kawai ke zaune a ciki.
Ko shakka babu, wannan tsari na kusanta gwamnati da jama’a da gwamnatin Dakta Dikko Umar Radda ta bullo da shi ya yi daidai da hangen nesa na wadanda suka kirkiro da tsarin sanya kananan hukumomi a mataki na uku na gwamnati. Hakan ya kara kusanto da jama’ar karkara kusa da gwamnati. Ana ganin tasirin hakan a zahiri.
A zahiri yanzu ana ganin shugabannin kananan hukumomin jihar Katsina suna gudanar da ayyuka raya kasa da suka hada da gina makarantu, dakunan shan magani, asibitoci, hanyoyin karkara, samar da ruwan sha, ayyukan noma, noman rani, shirye-shiryen kawar da fatara da talauci, da magance matsalolin tsaro.
Hakika Dikko Radda ya kwato kananan hukumomi a jihar Katsina daga matsalolin da suka dade a ciki wadanda suka sa suka yi mutuwar tsaye, tare da sake hura masu rai.
Mannir Shehu Wurma PhD, shi ne Shugaban Karamar Hukumar Kurfi