Kisan Masu Maulidi a Kaduna: Harkar Musulunci Ta Yi Allah Wadai da Kira a Dauki Mataki
- Katsina City News
- 06 Dec, 2023
- 587
Sanarwa Ga Manema Labarai
Harkar Musulunci Karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta yi Allah-wadai da kisan kiyashin da sojojin Nijeriya suka yi akan masu Maulidi a Tudun Biri.
Rahoto da ya zo mana cewa, sama da Musulmai 150 ne Sojojin Nijeriya suka yi wa kisan kiyashi a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.
An kai harin ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, 2023, ta hanyar amfani da jirgin yaki mara matuki.
Wata majiya mai tushe daga kauyen ta tabbatar da cewa ana taron bikin Mauludi, kuma daruruwan musulmi muminai a ciki da kuma na kusa da kauyen suka taru domin murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAWA). Sai dai abin takaicin shi ne Sojoji suka yi wa taron Maulidin ruwan bama-bamai.
A cewar wani ganau, harin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na dare, inda mutane suka garzaya domin kai agajin gaggawa. Bayan kamar mintuna 30 da harin farko sai aka sake kawo musu hari a karo na biyu.
Maulidin Manzon Allah (SAWA) ibada ce mai matukar muhimmanci a addinin Musulunci da take tunatar da musulmi soyayya da karantarwar Manzon Allah (SAWA). Saboda muhimmancinsa, musulmi suna shafe watanni da dama suna murnar maulidi.
A watan Satumbar 2023, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da dama a Nijeriya sun ayyana ranar Maulidi a matsayin ranar hutu. Wannan ya zama wajibi ga dukkan daidaikun mutane da kungiyoyi su san wannan muhimmin taro na bikin maulidi. A don haka harin da sojoji suka kai wa Musulmi masu ibada a Tudun Biri abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin Allah-wadai ne.
Jaridun kasar da dama sun ruwaito cewa sojojin Nijeriya sun dauki alhakin kisan gillar da aka yi a Tudun Biri wanda ya yi sanadin kashe daruruwan musulmi masu ibada a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Sojojin sun ce harin kuskure ne. Ya bayyana cewa irin wannan kisan kiyashi da ake kira na kuskure ya faru sau da dama a cikin wannan shekaru goma kadai, musamman a arewa maso gabas da arewa maso yamma. Ayyana wannan ta'asa a matsayin kuskure ba abin yarda ba ne. A don haka mun dora alhakin wannan kisan kiyashi akan Sojojin Njeriya.
Jami’an tsaron Nijeriya sun sha kashe fararen hula a matsugunai, sansanoni, kauyuka, da garuruwa da dama. A shekarar 2014 wani jirgin sojin Nijeriya ya jefa bam a kauyen Daglun na jihar Borno, inda ya kashe fararen hula 20. A shekarar 2015, sama da almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky 1,000 ne sojojin Nijeriya suka kashe a Zariya. A shekarar 2017, an kashe mutane 76 a harin da sojojin saman Nijeriya suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Rann a jihar Borno. A shekarar 2022, an bayar da rahoton cewa, an kashe mutane 64 a wani harin da sojojin Najeriya suka kai a kauyen Mutumji da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara. Wannan zalunci ne da ba za a amince da shi ba, kuma ba za a iya la’akari da su ba, kuma yin shiru a kan wannan ta’asa zai haifar da sake aukuwar wani kisan gilla.
Dangane da abin da ya gabata, Harkar Musulunci a karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta yi tir da kisan kiyashin da aka yi a Tudun Biri, tare da gabatar da bukatu kamar haka:
1) Duk mai hankali ya fito fili ya yi Allah-wadai da wannan ta'asa da neman a yi wa al'ummar Tudun Biri adalci.
2) A gano wadanda suka aikata wannan kisan kiyashi, a bincike su, a kuma hukunta su.
3) A gudanar da bincike domin gano adadin mutanen da aka kashe ko suka jikkata, da kuma asarar da mutanen Tudun Biri suka yi a sakamakon wannan kisan kiyashi.
4) Sojojin Nijeriya, gwamnatin jihar Kaduna, da gwamnatin tarayyar Nijeriya su biya diyya ga iyalan wadanda harin Tudun Biri ya rutsa da su.
Sheikh Sidi Munir Mainasara Sokoto a madadin Harkar Musulunci Karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Ya’qoub Zakzaky (H).