TANKO YAKASAI YA SHEKARA 98 A DUNIYA.
- Katsina City News
- 05 Dec, 2023
- 675
_Haruna U Jahun.
Yau Alhaji Tanko Yakasai OFR yake cika shekaru 98 a duniya. An haife shi ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 1925. Alhaji Tanko Yakasai ɗan siyasa ne na ainihi, ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam ne, tsohon kwamishinan a gwamnatin gwamna Audu Baƙo sannan Liason Officer ga shugaban ƙasa Marigayi Alhaji Shehu Shagari a jamhuriyya ta biyu.
Bayan ilimin addini da yake da shi ya samu karatun boko ta hanyar yaƙi da jahilci saboda ƙwazonsa da himmarsa a lokaci ƙanƙani ya iya rubutu da karatu sannan ya iya turanci wadda ya bashi damar tafiya ƙasar Rasha a shekarar 1960 inda ya yi diploma akan kimiyyar siyasa. Ko da yake a dawowarsa Nijeriya jami'an tsaro suka cafke shi a filin jirgin saman Legas a shekarar 1961 suka ƙwace certificate ɗin karatun nasa bisa tuhumar yaje ya yi karatu ƙasar da suke bin tsarin kwamisanci domin ya koyo dabarun juyin juya hali.
Alhaji Tanko Yakasai ya fara harkokin siyasa ne a shekarar 1951 inda ya shiga Jam'iyyar Neman Sawaba wato Northern Elements Progressive Union ko NEPU a taƙaice. Bisa ƙoƙarinsa da jajircewarsa ya National Publicity Secretary ɗin jam'iyyar na ƙasa. Sannan ya zama Edita na jam'iyyar a jaridar The Comet wadda Dr. Nnamdi Azikwe ya bawa jam'iyyar shafi a jaridar bayan ƙawancen da suka yi. Hasali ma dai Alhaji Tanko shi ya rubuta kudin tsarin jam'iyyar NEPU. A Jamhuriyya ta biyu yana daga cikin jiga-jigan da aka kafa jam'iyyar NPN da shi kuma bayan nasarar jam'iyyar ya zama mai baiwa shugaban ƙasa Shagari shawara.
Yana daga cikin ƴan siyasar da suka sha ɗauri kamar goro tun kafin ƴancin Nijeriya da kuma bayan samu a ƴanci domin tsakanin shekarar 1953 zuwa 1986 an ɗaureshi sau goma a lokuta daban daban. An ɗaureshi sau huɗu lokacin Turawan mulkin mallaka sannan an ɗaureshi sau huɗu a Jamhuriyya ta farko bayan ƴancin kai. Sai kuma sau ɗaya lokacin mulkin soja na Manjo Buhari da kuma sau ɗaya lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida.
Mutum ne haziƙi daya gabatar da muƙaloli a harshen turanci daban daban kamar ka ce dama can ɗan boko be ban da kuma laccocin siyasa wadda wannan da ma gonarsa ce. Ga kuma magana akan harkokin yau da gobe wadda har yanzu bai daina ba dukka yawan shekarunsa.
Ya je ƙasashen duniya sama da talatin (30) na Afrika da Asiya, da Europe da America ƙasashen da ya je sun haɗa da United States of America, Russia, United Kingdom, France, Germany, Italy, Spain, Japan, India, People's Republic of China, South Korea, Philippines, Malaysia, Indonesia, Hong Kong, Burma, Taiwan, Thailand, Sri Lanka, Brazil, Egypt, United Arab Emirates, Qatar, Saudi Arabia, Syria, Lebanon, Kenya, Tanzania, Ethiopia, Ghana, Guinea, Mali, Togo, Republic of Niger da sauransu.
Allah ya albarkaci Alhaji Tanko da lafiya domin duk da tarin shekarunsa amma hankalinsa da tunaninsa sunanan garau babu wani gigin tsufa ko birkiicewa. Zai baka labarin abubuwan da suka faru shekara casa'in tiryan-tiryan. Har yau idan wani abu ya shige mini duhu a Jamhuriyya ta farko ko ta biyu shi nake tuntuɓa domin ya warware mini. Al'amarin da kullum idan na ce masa Baba rayuwarka tana bani mamaki!! Sai yace wannan daga Allah ne.
Wani ƙarin mamaki hatta abubuwan zamani basu barshi ba. Ya na yin Facebook, yana WhatsApp domin ko shekaranjiya Lahadi 3/12/2023 ya turo mini wani tsokaci da ya yi ta WhatsApp akan halin da ake ciki a Nijeriya.
Allah ya ƙarawa Baba lafiya da nisan kwana
#Hoto: lokacin wata ziyara da na kai masa a gidansa na Kano shekara ɗaya da ta gabata.
Daga Haruna Uba