Shirin DIGIKAT: Ilimin Kwamfuta Kyauta A jihar Katsina
- Katsina City News
- 03 Dec, 2023
- 598
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Ana sa ran Al’ummar jihar Katsina miliyan hudu, za su ci gajiyar ilimin kwamfuta kyauta da ake yi a cikin harshen Hausa ta hanyar shirin DIGIKAT.
A yayin kaddamar da shirin a dakin taro na tsohon gidan gwamnatin Katsina Manajan shirin na DIGIKAT, Muhammad Abbas Usman ya bayyana kudirin shirin na samar da ilimin kwamfuta kyauta ga mutane miliyan hudu nan da shekarar 2027 masu zuwa.
Usman yayi cikakken bayanin cewa a yanzu haka an bude shafin yanar gizon shirin na DIGIKAT domin yin rijista, inda kashi na farko ana sa ran Mutum dubu 15,000, za su iya amfani da wayoyin hannu na Android don shiga gidan yanar gizo.
An yi ƙoƙari don haɓaka aiki a matakin farko ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa daga ma'aikatan gwamnati, malaman makaranta, da dalibai, da daidaikun mutane.
Muhammad Abbas Usman ya ci gaba da bayyana cewar shirin na DIGIKAT zai ba da fifiko ga wasu fannoni da suka hada da shirye-shiryen kiwon lafiya ta wayar salula, koyar da dabarun noma na zamani, da magance wasu muhimman al’amura na rayuwa.
Da yake wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, Daraktan Yada Labarai, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua, ya yabawa matasa bisa goyon bayan kokarin gwamnati, yana mai bayyana su a matsayin masu bayar da gudummawar ci gaba.
Manyan mutane da suka hada da mai ba da shawara na musamman kan shirin, Dokta Muttaka Rabe Darma, Sirajo Aliyu (Mataimakin Farfesa) kuma shugaban kungiyar masu sarrafa na’urorin kwamfuta ta kasa, Dakta Bashir Kurfi, shugaban shirin DIGIKAT Usman Ishak Karofi, da Sanusi Muhammad Sulaiman. Abdulrahman Mustapha, da Adnan Muhammad, sun bukaci al’ummar jihar Katsina da su yi rajistar shirin, su kuma ba da gudunmuwarsu domin samun nasarar shirin.
www.digikattraining.com.ng ko a sauke manhajar su a Play store don shiga tsarin