Tawagar Lauyoyi Masu Zaman Kansu Kimanin 200 Sun Kudiri Aniyar Taimakawa Abba Gida Gida A Kotun Ƙoli
- Katsina City News
- 03 Dec, 2023
- 524
Kimanin Lauyoyi 200 ne masu zaman kansu daga jihohin Arewa 19 suka sadaukar da kansu Domin taimakawa Gwamna Kabir Yusuf na jihar Kano don samun nasara a ƙarar da ya shigar a Gaban Kotun Ƙolin Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai a Arewa House, A Yau Lahadi a Kaduna, Mai magana da yawun lauyoyin, Yusuf Ibrahim, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kotun koli da kada su bari Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya ɗaya, Yana mai cewa al’ada ce ta dimokuradiyya mara kyau.
Lauyoyin sun dage cewa dole ne a bi doka don tabbatar da kuri’un kowane dan Najeriya a lokacin zabe.
Sun kuma bayyana goyon bayansu ga Abba K Yusuf yayin da suke bayyana cewa hukuncin da Kotun Ɗaukaka Kara ta yanke babu adalci a cikinsa
KBC Hausa News