An Kama Tsohon Shugaban Hukumar NIRSAL Bisa Zargin Almundahana Da Sama Da Faɗi....
- Katsina City News
- 27 Nov, 2023
- 638
Kimanin tsawon shekara guda kenan da korar Shugaban daga kan Muƙamin shi na Managing Director of the Nigeria Incentive-Based Risk Sharing System for Agricultural Lending (NIRSAL), Aliyu Abdlhameed, an kama shi da zargin wawure Maƙudan Kuɗaɗe wuri na gugar wuri har Naira Bilyan Biyar da Milyan Ɗari Shidda N5.6bn da aka ware domin noman Alkama.
Shidai Shirin NIRSAL, wata hukuma ce wadda aka ƙirƙiro daga babban bankin Najeriya wadda ba banki bane, amma an ƙirƙira shi domin kulawa da abubuwan da suka shafi asarorin manoma an kuma ware Dalar Amurka milyan Ɗari Biyar $500m domin gudanarwar hukumar.
An dai sallami Abdulhameed daga Muƙamin sa ne bayan da ƙwamitin Zartarwa na Babban Bankin Najeriya CBN yayi bincike akan batun cin hanci da rashawa dake kanshi wanda aka sallame shi a watan disambar Shekarar da ta gabata tare da zargin salwantar da kuɗin noman Alkama a Shekarar 2018 wanda kuɗin suka kai N5.6 billion an ware su domin manoman Alkama a jihohin Kano da Jigawa.
An dai kama shi a Ma'aikatar tattara haraji ta ƙasa dake Abuja a satin da ya gabata Inda ake zargin yaje kamun ƙafa domin a sake maida shi kan Muƙamin shi.