JAMI 'AN "COMMUNITY WATCH" SUN FAFATA DA ƳAN BINDIGA . ...sun kashe wasu .wasu sun sha da kyar

top-news

Misbahu Ahmad Batsari
@ Katsina Times 

Jami'an tsaron "community watch corps"sun fafata da ƴan bindiga a yankin Batsari ta jihar Katsina.

Da misalin ƙarfe 9:30pm na daren asabar 25/11/2023. ƴan bindiga masu tarin yawa suka kaima jami'an tsaron community watch corps dake aikin bada tsaro a ƙauyen Watangaɗiya hari.

Yan bindigar  Sunyi ƙoƙarin yima jami'an tsaron ƙawanya amma  jami an da hadin gwiwar mutane  garin suka dake akayi ta ɗauki ba daɗi, inda ƴan bindigai suka dinga antaya masu harsasi  da bindigar girke ,wasu kuma da AK-47,kamar yadda wani mutumin garin ya tabbatar da jaridun Katsina Times.

Yan ta addar sun fi yan community watch manyan makamai da  yawa amma  duk da haka suka dage aka  ɗauki lokaci ana fafatawa 
Da barayin suka lura ba sa a, sai suka janye ,jikin su tare da daukar gawarwakin yan uwansu da aka kashe.

Da ƙura ta nutsa, jami'in tsaro ɗaya ya samu rauni, sannan sun sace babura huɗu, su kuma ɓarayin sun bugo wayar da suka sace  sunce an kashe masu mutum uku.

Katsina Times 
@www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
Www.taskarlabarai.com 
07043777779 08057777762

NNPC Advert