Ana zaman dar-dar a Kano yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da na NNPP Zasu Gudanar Da zanga-zanga A Ranar Asabar.
- Katsina City News
- 23 Nov, 2023
- 749
Da yake yiwa manema labarai jawabi a Yau Alhamis a Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa dake Abuja, Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben Gawuna/Garo, Rabiu Suleiman Bichi, Wanda ya jagoranci Sauran masu Ruwa da tsaki da suka haɗa da ‘yan Majalisar dokokin jihar Kano, Tsofaffin kwamishinoni, Tsofaffin mashawarta na musamman. da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar, Yace yayin da jam’iyyar NNPP zata Gudanar da zanga-zanga a Kano a Ranar Asabar, APC za ta shirya Gagarumin gangami a Ranar.
Bichi yace bayanan da suka samu sun nuna cewa masu Ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP sun tsayar da wata Gagarumar zanga-zanga Ranar Asabar bayan sun gana da jagoransu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sai dai ya dage cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC suma za su Gudanar da babban taro a Kano a wannan rana, Domin nuna Goyon bayansu ga Ɗan Takarar jam’iyyar APC Nasiru Gawuna.
Da yake amsa tambaya kan yiwuwar barkewar rikici, ya ce, “Mu ’yan kasa ne masu bin doka da oda, Kuma ba za mu yi wani abu don kawo cikas ga zaman lafiya ba, Amma ba za mu yi kasa a Gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyinmu.
“Al’amura na kara ta’azzara tun bayan da Shugaban jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo Kano ranar Lahadi, inda ya Gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.