"Cikin dan lokacin da Muka yi a Majalisar Wakilain Nigeriya na samarwa Matasa 92 Aiki a matakai daban-daban" Aminu Chindo

top-news



 
Zaharaddeen Ishaq Abubakar

A wata tattaunawa da Katsina Times ta yi da Hon. Aminu Ahmed Chindo (Sadaukin Katsina I) Tsohon Danmajalisar Tarayya mai wakiltar Karamar hukumar Katsina a majalisar wakilai ta Najeriya, bayan hukuncin Kotun daukaka kara ta bayyana Abokin Takarar sa daga Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe.

Hon. Aminu Ahmed Chindo ya mika godiyarsa ga Al'ummar Jihar Katsina musamman na karamar hukumar da ya wakilta wato Katsina ta tsakiya.

Chindo ya mika godiyarsa a madadin iyalan Alhaji Amadu Chindo, yace yaji dadi kwarai da gaske akan Soyayya da al'ummar karamar hukumar Katsina ta nuna mashi wanda hakan ya kaishi ga Nasarar lashe zaben a rumfunan zabe 499 cikin 501.  yace wannan ya nuna al'umma suna tare da mu.

Yace "Ina godiya ga Al'ummar Karamar hukumar Katsina, Malamai da Matasa Maza da Mata da suka bada goyon baya da Addu'a Nagode kwarai da gaske" ya bayyana.

Honorable Chindo yace "Mun dauko Alkawari kuma mun cika, ina Alfahari da hakan." Yace "Munci zabe mun je majalisar Nijeriya kuma mun kokarta mun samu Kwamiti mai karfi da ya taimaki al'ummar karamar hukumar Katsina." 

Chindo yace "Cancanta yasa aka bani Chairman na Interior Internal Security a Nigeria wanda hakan ya bani damar samar wa matasa Aiki na Immigration, Civil Defence, da sauran Ayyuka ga Matasan har 92."

Yace "Na samu kaina mai tausayin Al'umma a lokacin da aka kwace kujerar Majalisar Taraayya daga wajena aka bawa wanda ake so, ko babu komai damar da al'umma ta samu ce wadda ba a taba samun irinta ba shekaru ashirin baya, ace Dan majalisar Dokokin Tarayyar Nigeria a cikin wata biyar da fara aikin Majalisa ya samarwa matasa 92 Aiki, ba a taba irin wannan ba." 

Yace "har yau har gobe ba zan daina bautawa al'ummar jihar Katsina ba, kuma ya isa misali cewa duk da sun amshe kujerar amma a haka sai da na samarwa mutum 11 Aiki yanzu haka sun tafi."

Aminu Chindo yace kishi ne da son mutanen Katsina yasa nake wannan fafutukar, sabanin wasu idan sun samo damar daukar aikin sai su sayar. Yace shi kuma ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kawo sauyi ga matasa don su samu aikin yi.

Honorable Aminu Chindo ya bayyana cewa "har mai girma Gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda na taimaka masa ta hanyar rage masa Matasa masu zaman banza a jihar Katsina, kuma muna daukar kowa da kowa, babu ruwan mu da jam'iyya ko wani abu, dama wannan yana daga cikin irin tunanin Gwamna Dikko Umar Radda."

A karshe Honorable Aminu Ahmed Chindo ya yiwa masoyansa Albashir da cewa Siyasa yanzu ya fara, babu ja baya yanzu zai ci gaba da gwagwarmayar Siyasa, yace kuma akan gaskiya babu wanda ba zai iya fadawa gaskiya ba idan yaga anyi ba daidai ba sai ya fada don a gyara.

NNPC Advert