GOMNA RADDA YA GABATAR DA KASAFIN KUDIN SHEKARAR 2024 A GABA ZAURAN MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KATSINA
- Katsina City News
- 16 Nov, 2023
- 788
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya gabatar kiyasin kudi na Naira 454,308,862,113.96 a matsayin tayin dokar kasafin kudin shekarar 2024.
Kasafin kudin 2024 yayi nuni da cewa an kara samun karuwar N153,675,604,150.96 bisa ga kasafin kudin shekarar 2023.
An ware N 188,061,977,186.28 a matsayin kasafin kudin gudanar da al'amurran yau da kullum ( recurrent expenditure).
A bangare guda kuma zunzurutun kudi N 329,979,518,595.97 aka ware domin gudanar da manyan ayyuka ( Capital Expenditure).
Kasafin kudin ya bayyana wuraran da suka fi samun kaso mafi tsoka kamar haka:
Bangaran samar da ingantaccan ruwan sha: N67,161,802,447.30
Bangaran harkokin bunkasa Ilimi: N66,422,889,400.20
Bangaran ayyuka (works): N53,482,733,251.59
Bangaran kiwon lafiya: N 38, 326,241,171.23
Bangaran inganta muhalli : N 37, 700,116,210.24, sai
Bangaran harkokin noma: N20,513,909,753.71
A jawabin sa Gwamna Radda ya jaddada kudirin gwanatin sa wajan magance sha'anin tsaro, yana mai bayyana cewa gwamantin jiha hadin gwiwa da kananan Hukumomi sun ware Naira Biliyan 7 domin inganta harkokin tsaro ta hanyar tattara bayanan sirri, da daukar jami'an tsaro gami da horas dasu.
A nasa Jawabin, Shugaban Majalisar Dokoki Rt.Hon Nasir Yahaya, ya taya gwamna Radda murnar gabatar da kasafin kudi gamsashshe wanda ya kunshi muhimman abubuwan da al'umma ke bukata.
Ya bada tabbacin cewa Majalisa zatayi nazari dangane da kasafin kudin domin a amince dashi ba tare da bata lokaci ba domin tunkarar harkokin tsaro da kyautata rayuwar al'umma.
Katsina Trends