SHI KARATU MABUDIN ARZIKI NE ...Certificate kuma kawa ne..
- Katsina City News
- 16 Nov, 2023
- 677
Daga Abdurrahman Aliyu
Abubuwa da yawa na kai koma dangane da karatu da kuma kwalin sheda har wasu na danganta mai sana'ar acaba da kwalin shedar digiri, wanda a ganinsu kamar hakan kaskantar da Ilimi ne ace ana da kwalin sheda amma ba a aiki an koma sana'ar acaba.
Kwanakin baya kuma naga wasu na korafin saboda me wanda ba aikin koyarwa zai yi ba zai yi karatu har matakin Dakta? Duka masu wannan tunanin suna da tsukakkar fahimta ce kan alfanu ilimi da kuma darajar da Allah ya ba ilimi.
Shi karatu a ko'ina yana zama kofa ta arziki ne ga mai yin sa, a yayin da kwalin shedar da ya samu yake zama kawa a rayuwarsa, ko dai ya taimakai ya samu aikin gwnatin da suke kallon kamar wajibi ne ga mai digiri ko kuma ya kawata masa rayuwarsa ta fuskar lamurran da ya sa gaba na sana'a ko kasuwanci.
Amma duk wanda ya sa karatu da neman Ilimi gaba lallai ba zai yi talauci ba, kuma kansa ba zai kulle ba balle hassada da bakin ciki ko jin zafi ya samu fagen zama a ciki, rayuwarsa baki daya zata zama fitila ce ga abinda ya sa gaba.
Ina ba matasa shawara da mu dukufa wajen yin karatu da maida hankali wajen gina rayuwarmu ta fuskar neman ilimi da yada sa. Mu ziyarci masallatan unguwarmu da zaurukan malamai wajen daukar karatu. Mu yi karatun boko har matakin digirin-digir ko da ba ma aikin gwamnati.
Wani karamin misali da zan bada a karin kaina mun nemi wani aikin fassara mu ashirin, an zabo ni a matsayin mai karatun Ph.D an bani aiki fassara shafi 27 akan miliyan biyu, yayin da aka dauki sauran su goma 19 aka basu irin aiki nawa akan dubu talatin-talatin kacal, kuma aka sake ban aikin duba nasu aikin akan dubu goma-goma kowannensu.
Wannan ya faru ne sakamakon karatu da nake da shi sama da nasu. Wani karin misalin wani makwabci na ya taba sallama man yana tambayata don me zan tafi karatun Ph.D bayan bani aikin gwamnati? Me karatun zai tsinana man? Ban ba shi amsa ba. Amma a tsawon shekaru sama da ashirin da ya shafe yana aikin gwamnati da HND har zuwa yau din nan bai kamo kafa ta arziki ba. Ina son in sheda mai cewa arziki a cikin neman ilimi yake ba aikin gwamnati ba.
NB
Wannan hoton dake kasa na saka shi ne a matsayin misalan matasan da suke karatu zurfan ba tare da aikin gwamnati ba. Kabir Sa'idu Bahaushe na gab da kammala karatun digirinsa na biyu kuma ya dora sanwar tafiya na uku ba tare da yana aikin gwamnati ba, sai ni da nake gaf da kammala Digiri na uku ba tare da aikin gwamnatin ba. A haka kuma muka jagoranci ayyuka da dama da suka samar da sauyi ga ma'aikatan gwamnati da dama. Ya zuwa yanzu kuma dukkan mu CEO ne a wasu harkoki mabambanta.
Za mu cigaba da karatu har zuwa lokacin da lumfashinmu zai zo karshe a duniya.
Abdurrahman Aliyu marubuci ne kuma Malami a jami ar Umyu Katsina