JAM IYYAR PDP A KATSINA TA FADA SABON RIKICI. ....Wake da hannu a ciki?

Muazu Hassan
@ Katsina Times 

Yanzu haka jam iyyar PDP a jahar Katsina ta shiga sabon rikici akan nadin sabbin shugabannin kananan hukumomi na riko, kamar yadda uwar jam iyyar ta kasa ta nemi a yi.

Wani Dan Kwamitin shugabannin riko, Wanda uwar jam iyyar PDP  ta nada karkashin jagoranci Abdurraham Usman, sun tsara kowace karamar hukuma, masu ruwa da tsaki na jam iyyar daga matakin karamar hukuma zuwa na unguwanni, zasu zauna da yan jam iyyar domin zabo wadanda za a ba shugabancin na kananan hukumomi.

Dan Kwamitin ya shaida ma jaridun Katsina Times cewa, "mun saka ranar asabar da lahadi 18 da 19 na watan Nawumba, zamu hadu da duk masu ruwa da tsaki na jam iyyar domin tattauna abubuwa daban daban ciki har da gabatar da sabbin shugabannin jam iyyar na riko a matakin kananan hukumomi." Yace

"Kwatsam sai muka ji, za a gabatar da taron gabatar  shugabannin a ranar 13 ga Nawumba."

Dan Kwamitin yace "kaje ka duba faifan bidiyon taron Wanda shafin jaridar Taskar labarai ya sanya da hotunan da bidiyon akwai wasu dattawan jam iyyar a ciki akwai masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi  akwai Wakili daga uwar jam iyya ta kasa? amsa itace Babu! Me yasa basu amince da taron ba? Kuma anyi shi ba yadda aka tsara ba, ba a kammala tattara sunayen shugabannin daga kananan hukumomi ba." 

Hatta a gabatarwar babu jadawalin sunayen wadanda aka nada daga kananan hukumomi ba kuma takardun nadin su da akayi.
Taro ne kawai da aka tara, ba tsari, ba kuma takaimaiman nasarar abin da aka cimmawa kamar yadda wasu yan kwamitin suka bayyana.

Katsina Times ta gano kananan hukumomi 23, cikin talatin da hudu basu amince  da wadanda aka sanya sunayen su ba a matsayin sune shugabannin riko na kananan hukumomin su.

Katsina Times ta gano kananan hukumomi 20 an canza asalin sunayen da aka bayar a matsayin shugabannin riko na yankin su.

Katsina Times ta ga wata takarda wadda karamar hukumar Jibiya ta rubuta wadda tayi Watsi da sunayen da aka sanar a matsayin sune shugabannin su. Takarda wadda masu ruwa da tsaki na PDP a Jibiya suka sanya ma hannu sun ce sam an canza wadanda suka bayar.

Wani Dan Kwamitin shugabancin jam iyyar na jaha ya fada ma jaridun Katsina Times cewa, ganin ana abin da bai dace ba yayi niyyar ajiye mukamin shi har ya rubuta takardar shi, amma aka lallashe shi.

Duk wannan tirka tirka wa ake zargin ya jawo ta? Jaridun Katsina Times sun yi Magana  da mutane ashirin manya a jam iyyar PDP ta Katsina, dukkanin su, zargin da suke shine tsohon Dan takarar gwamna a  PDP, sanata Yakubu lado ya ke kitsa duk abin dake faruwa a jam iyyar.

Wadanda akayi magana dasu, suna zargin Yakubu lado yana son rike jam iyyar da duk abin da zai faru a cikin ta har 2027 domin ya sake takara.

Suna zargin ana son mayar da jam iyyar PDP ta Mutum daya a jahar Katsina, Suna zargin hatta shirya taron kaddamar da shugabannin na riko Wanda ba a yi shi akan Kaida ba, duk shi Yakubu lado ne ya shirya shi.

Katsina Times ta zanta da sanata Yakubu lado inda ya karya ta duk zarge zargen, Yakubu lado ya bayyana ma jaridun Katsina Times cewa shi cikakken Dan jam iyyar PDP kuma yana  da hakki a cikin ta.

Yace yayi takara a jam iyyar har sau biyu, don haka yana da mutane kowace karamar hukuma yace kila su aka gani a jadawalin sunayen aka dauka shi ya sanya su.

Zargin shine ya bada kudin da akayi taron shima ya karyata, yace a tambayi shugabannin rikon a ina suka samo kudin  su. yace jam iyya ta mutane da yawa ce kuma kowa na iya bada gudunarwar sa

Katsina Times 
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar Taskar labarai 
@ www.jaridartaskarlabarai.com 
07043777779  08057777762