Rubaɗo ya roƙi ƙungiyar Kwadago ta janye yajin Aiki
- Katsina City News
- 15 Nov, 2023
- 622
Nuhu Ribadu Ya Bayyana Takaicinsa Kan Harin da aka kaiwa Shugaban Kwadago Ya Roke dasu janye Yajin Aikin da suke.
Mai Baiwa Shugaban ƙasa Shawara kan Harƙoƙin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan harin da aka kai wa Shugaban Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) Joe Ajaero a Owerri, A Babban birnin jihar Imo, a Ranar 1 ga watan Nuwamba.
Ajaero, Wanda ya jagoranci zanga-zangar zuwa Owerri, an yi masa mummunar duka tare da tsare shi na sa’o’i. Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a tsakanin kungiyoyin kwadago, lamarin da ya sa suka bayar da wa'adi na neman a kamo maharan Ajaero tare da yin barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar idan ba a biya musu bukatunsu ba.
Gwamnatin tarayya a kokarinta na ganin ta dakile yajin aikin, ta nemi kotu ta ba da umarnin hana kungiyoyin kwadago ci gaba da yajin aikin. Sai dai yajin aikin ya fara ne a ranar litinin din da ta gabata, lamarin da ya kawo tsaiko a duk fadin kasar.
A wata sanarwa da ya fitar a Yau Laraba Nuhu Ribadu ya Buƙaci kungiyar kwadago da ta sake duba matakin da ta dauka na yajin aikin, Yana mai jaddada cewa an kama wadanda suka kai harin Ajaero, kuma ana cigaba da bincike.
“Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya damu matuka da ayyana yajin aikin da shugabannin kungiyoyin kwadagon karkashin jagorancin NLC da TUC suka yi a fadin kasar,” inji Ribadu.
Hukumar ta NSA ta bayyana damuwarta ta musamman game da irin tasirin da yajin aikin zai yi ga rayuwar talakawan Najeriya da kuma yadda ya shafi tsaro da tattalin arziki da sauran muhimman muradun kasa.
Da yake jawabi ga shugabannin NLC, Ribadu ya amince da damuwar kungiyar kwadago tare da tabbatar da aniyar Gwamnatin tarayya na magance su ta hanyar tattaunawa mai ma’ana.
“Kamar yadda shugabannin NLC suka shaida, nan take NSA ta shiga tsakani bayan samun labarin faruwar lamarin da ya shafi shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Kwamared Joseph Ajero, wanda aka kaiwa hari a Owerri, jihar Imo,” Ribadu ya bayyana.
“Hukumar NSA ta yi nadamar faruwar lamarin tare da yin Allah-wadai da lamarin gaba daya domin ya sabawa doka da ka’idojin ‘yancin yin tarayya da fadin albarkacin baki da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnatinsa suka bi”.
Da yake jaddada kudirin gwamnati na tabbatar da doka da oda, Ribadu ya tabbatar wa kungiyar kwadago cewa za a hukunta wadanda suka kai harin kan Ajaero.
“Gwamnatin Tarayya ba za ta taba lamuntar irin wannan aiki ba,” in ji shi.
“Sakamakon afkuwar lamarin, an umurci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da Gurfanar da waɗanda suka aikata laifin, bayanai da ake samu sun nuna cewa an riga an kama wasu a kan haka, Sakamakon binciken zai fito. a sanar da jama’a da zarar an kammala shi”.
KBC Hausa News