GASKIYAR LAMARIN TASHIN SOJOJI A WAGINI
- Katsina City News
- 10 Nov, 2023
- 777
Misbahu Ahmad @Katsina Times
Da yammacin ranar alhamis 09-11-2023, kwatsam sai mutanen Wagini suka ga sojojin dake garin na kwashe kayan su, wannan yasa aya tambaya daga mafi yawancin al'umma.
Binciken Katsina Times ya tabbatar mana da cewa, an umurci sojojin su tashi daga wagini su koma wani gari dake can yammacin wagini watau Nahuta.
kamar yadda wani mai ruwa da tsaki a harkar tsaro a yankin ya bayyana mana, sojojin na Wagini sun koma Nahuta bisa umurnin da aka basu amma daga bisani an dawo da su a matsugunnin nasu dake Wagini domin su cigaba da bada gudummuwar su a garin, inda yace jiya Alhamis aka kwashe su zuwa Nahuta amma yau Juma'a da sanyi safiya aka dawo da su garin na Wagini.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762