Za'a kaddamar da wajen koyar da gyaran matoci na zamani a Katsina
- Katsina City News
- 09 Nov, 2023
- 711
Daga Muhammad Kabir, Katsina
Babban daraktan ma'aikatar hukumar bunƙasa ƙera motoci ta Nijeriya "National Automotive Design And Development Council" Mista Oluwemimo Joseph Osanipin, ya ziyarci kungiyar kanikawa reshen jihar Katsina.
A yayin ziyarar mista Joseph yayi albishir ga kungiyar kanikawan na samar da kayayyakin aikin koyarwa na zamani, tare da kaddamar da cibiyar nan da yan kwanaki masu zuwa.
Mista Joseph ya muna jin dadin sa bisa yadda ƴan kungiyar suka tarbe shi hannu biyu.
Shima a nashi jawabin shugaban kungiyar kanikawa reshen jihar Katsina injiniya Abbati Muhammad, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa injiniya Sani Halilu ya nuna jin dadin sa a kan ziyarar.
Halilu ya yaba ma shugaban "Nigeria Talent Exploration Challenge" Arch. Faisal Jafar Rafindadi, bisa yadda ya jajirce wajen samar ma al'umma ayyukan yi.
Halilu ya kara da cewa idan matasa suna da abin yi, matsalolin ƙasar zasu ragu da kaso 95%.
"ƙungiyar NATA na taka muhimmiyar rawa a ƙasarnan."
"Manufofin wannan kungiyar ta NATA shine samar ma matasa ayyukan yi, domin su dogara da kansu".
Daga karshe yayi addu'a ga babban daraktan da yan rakiyar sa, tare da fatan Allah ya maida su gida lafiya.