Yan Siyasa Ne Suka Haifar Da Matsalolin da Ake Ciki A Najeriya Cewar Buratai
- Katsina City News
- 04 Nov, 2023
- 513
Tsohon Hafsan Sojin ƙasa Laftanar Janar Tukur Buratai ya zarge Ƴan Siyasu da haifar da Rashin tsaro da sauran matsalolin da Suka addabi ƙasar a halin yanzu.
Buratai, wanda ya bayyana hakan a wata lacca da aka Gudanar a Jami’ar Ibadan a Jiya Juma’a, Yace ‘yan siyasa sun shafe shekaru da dama suna karkatar da Kuɗaɗen jama’a tare da shiga ayyukan almundahana, wanda hakan ya sa jama’a suka yi watsi da Amana da kuma kawo cikas ga cigaba. Ya kuma zarge su da yin manyan alkawura a lokacin yakin neman zabe amma da wuya su Iya cika ɗaya daga cikin alƙawurran da suka dauka.
“Rashin tsaro da ake fuskanta a kasar nan tun Shekarar 2009 shi ne samar da ajin siyasa,” inji Buratai. "Tare da karfi na siyasa, za a iya wuce gona da iri."
Buratai ya kuma yi kakkausar suka ga masu suka da suka yi ta kiraye-kirayen a kore shi a lokacin da yake kan karagar mulki, inda ya ce bukatunsu ya dogara ne da son zuciya ba wai tantance kwazonsa ba.
Kalaman na Buratai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro da dama da suka hada da ta'addanci, fashi da makami, da kuma Garkuwa da mutane. Ana sukar Gwamnati kan yadda take tafiyar da waɗannan kalubale, inda ‘yan Najeriya da dama ke zarginta da rashin inganci da cin hanci da Rashawa.