Kashe tsohon Kantom a Zakka: Kungiyar Cigaban Al'umma ta Zakka ta Barranta, kuma ta bayyana shi a Mutumin Kirki
- Katsina City News
- 03 Nov, 2023
- 936
Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Wata kungiya mai suna Zakka Community Development Association ZACODA bisa Jagorancin Shugaban Kungiyar Malam Musa Usman Zakka Dattijo mai shekaru 60 da Al'ummar Zakka suke girmamawa ya bayyana matsayarsu akan Kisan da a ka yiwa Hon. Hamza tsohon Kantoman Karamar hukumar Safana wanda sabbin jami'an sakai na Dikko Radda sukai masa bisa zargin yana bada bayanai ga barayin daji.
Musa Usman Zakka da yake zantawa da manema labarai a Sakatariyar kungiyar 'Yan jaridu ta jihar Katsina ya bayyana cewa kungiyarsa da Al'ummar Zakka basu da Alaka da wannan kisa, kuma a iya saninsu Hamza bashi da wani abu na fadi a wajen su. Yace "koda dai a wani labarin Musa Zakka ya ce akwai wani lokaci da ya taba yunkurin neman belin wasu matasa da ake zargi suna cikin masu garkuwa da mutane, yace "amma dai mu kam bamu san komai daga gare shi ba"
Abdulhamid Danjuma tsohon Kansila daga Zakka kuma Kansila mai ci a yanzu, Babban Abokin Marigayi Hamza da aka kashe yace, tare suka tashi da Hamza sunyi Makarantar Firamare tare, kuma suna shawartar juna a koda yashe, ya bayyana cewa bai san wani Aibi da marigayin keda shi ba, yace ba'a zagin Hamza gabansa shima ba a zaginshi gaban marigayi Hamza. Ya bayyana cewa, su abinda suka dauka karar kwana ce tazo kuma hamza tashi ce ta kare saidai fatan Allah ya jikansa da Rahama, yace amma akwai zarge-zage da iyalansa sukai marasa tushe wadanda kusan karairayi ne a ciki. Idan za'a iya tunawa kimanin kwanaki 9 da suka gabata ran 25 ga watan Oktoba aka wayi gari da kisan tsohon Shugaban ƙaramar hukumar wanda ya bawa kowa mamaki, kamar yanda Iyalan sa suka bayyana cewa tun kafin a kasheshi sun samu labarin jami'an sa kai da aka yaye sunce zasu kashe Hamza da shi da dansa guda daya, sunyi kokarin daukar duk wani mataki da shi kansa Marigayin amma a karshe dai saidai suka aikata kisan, matar Marigayin ta ce "sun shigo har cikin gida suka farfasa mana kayayyaki suka cinye mana abincin da ya rage dafaffe a gidan sana suka ja mai gidanmu suka tafi dashi wajen gari suka harbesu a kai da kafada da kuma kugu, kuma suka hana ayi masa jana'iza".