AN KASHE WADANDA AKE ZARGI DA INFOMA A ZAKKA.
- Katsina City News
- 25 Oct, 2023
- 918
@Katsina Times
Sabbin yan sintirin da aka dauka aiki Kwanan nan, sun kama wasu infoma guda uku a zakka ta karamar hukumar Safana.
Majiyarmu tace,wadanda ake zargin da suna baiwa barayin dajin hadin kai sune Bello Sabon Dawa, Wanda yake rike da mataimakin shugaban jam'iyyar APC a Zakka 'A'.
Na biyu shine, Hamza Zakka Tsohon Kantoma a Tsohuwar Karamar Hukumar Zakka da aka taba kirkira aka rusa tun lokacin da Marigayi Umaru Musa Yar'adua yana Gwamna.
Na ukun su , an sanshi da sunan Lawal Zakka.
Majiyarmu tace, Mutanen gari suka kai korafin mutanen wajen sabbin yan Sintirin da cewa suna tarayya da Ƴanbindiga kuma suna basu bayanan mutane.
Yan Sintirin sun kama su da binciken su, daga baya aka ga Gawarwakin su a wajen garin Zakka.
Lamarin ya faru a tsakanin ranakun Litinin 23/10/2023 da Talata 24/10/2023.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762