ILIMI: Gwamnan jihar Katsina ya biya fiye da Naira Miliyan ɗari shida, Tallafin Karatu ga Ɗaliban Kwalejojin jihar
- Katsina City News
- 24 Oct, 2023
- 620
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times, 23,10,2023
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya a cikin a yunkurin sake farfado da harkar ilimi a jihar Katsina, ya kaddamar da shirin kawo sauyi na Sama da Naira miliyan 600, alawus-alawus na tallafin karatu ga daliban da ke manyan makarantu daban-daban a jihar. Wannan yunƙuri ya bayyana jajircewar gwamnan wajen inganta harkokin ilimi a jihar Katsina.
Taron kaddamar da bayar da Tallafin ya gudana ne a harabar hukumar bayar da tallafin karatu ta jihar Katsina, inda Gwamna Radda ya kuma ba da lambar yabo ta “Maiden Katsina Award of Academic Excellence to Students with Higher CGPA (4.50 and Sama), A turance. Wannan karramawar dai wata sheda ce ta kara himma ga Dalibai don suyi kokari, da kuma haskawa 'yan baya.
Gwamna Radda ya bayyana aniyarsa na kyautata rayuwa ga hazikan dalibai masu ƙwazo da ƙwararrun ɗalibai, da nufin rage wa iyaye matsalolin tattalin arziki a jihar. Haka kuma Gwamnan ya sanar da amincewa da N640,648,546 don biyan tallafin karatu ga ɗalibai na shekarar 2020/2021 da 2021/2022. Wannan tallafin karatu zai amfanar da daliban Katsina masu neman ilimi kai tsaye, tare da samar da kyakkyawar makoma.
Haka zalika Gwamna Radda ya bayar da kyautar kudi ga dalibai na musamman na Katsina wadanda ba su gaza 210 ba da maki CGPA da ya kai 4.5 zuwa sama. Daliban da suka kware, wadanda suka yi karatu a jami’o’i, da kwalejin kimiyya da fasaha, da kwalejin Gwamnatin tarayya ta FCE, ana ganin hakan zai kara karfafa Daliban da kuma kara habbaka gasa a tsakaninsu
Gwamna Radda ya kuma bayyana shirin gina makarantun na musamman domin yara marasa galihu masu hazaka daga cikinsu, domin gogewa da shiga tsara kamar yanda 'ya'yan masu hannu da shuni zasuyi.
Dangane da wannan kokari Kwamishinan ma’aikatar fasaha da koyar da sana’o’i na jihar Katsina, Farfesa Abdulhamid Ahmad ya bayyana jin dadinsa kan yadda Gwamna Radda ya yi kokarin samar da guraben karo karatu da kwazon ilimi, yace: "Sashen ilimi na Katsina na samun gagarumin sauyi a karkashin jagorancin sa."
Dokta Aminu Salisu Tsauri, Sakataren zartarwa na Hukumar bayar da tallafin karatu ta Jihar Katsina, ya mika godiyarsa ga ‘yan Majalisar Dokoki na jihar Katsina da suka tallafa wa shirin gwamnatin Katsina ta hanyar tallafa wa dalibai a yankunansu da kudaden karatu. "Wannan kokari na hadin gwiwa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ilimi da kuma samar da kyakkyawar makoma ga matasan Katsina." Injishi.