Ba a kafa NBC don takura wa kafafen yaɗa labarai ba - Idris
- Katsina City News
- 12 Oct, 2023
- 746
Daga Shafin Film Magazine
MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC) da ta rungumi masu harkar yaɗa labarai domin a binciki dokokin karya ƙa'idojin yaɗa labarai.
Ministan ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyarar yini ɗaya a hedikwatar hukumar a Abuja.
Ya ce akwai buƙatar a sake saisaita alƙiblar hukumar ta yadda za a daina yi mata mummunar fassarar cewa ba ta da wani aiki ko amfani sai ƙaƙaba takunkumi, cin kafafen yaɗa labarai tara ko garƙame su.
Ya ce: "Ni ban yi amanna da cewa NBC ba ta da wani aiki sai cin tarar kafafen yaɗa labarai ba. Saboda a duk lokacin da ka ji an yi maganar NBC a labarai, ba za ka ji komai ba sai batun wani gidan talbijin ko gidan rediyo ya karya doka.
"Amma ni ina ganin cewa ba a nan ya kamata a tsaya ba. Akwai buƙatar a wayar wa jama'a da kai sosai. A kan haka, ina ganin ba a taɓuka wani ƙoƙari wajen isar da saƙo ga jama'a.
"Wajibi ne ku ƙara azama sosai, ta yadda mutane za su gane ku, kuma su fahimci irin ayyukan da su ka rataya a wuyan NBC, ba don komai ba sai saboda mutane ba su san waɗansu ayyukan NBC ba sai ƙaƙaba takunkumi, cin tara da garƙame kafafen yaɗa labarai.
"Ya kamata NBC ta himmatu wajen wayar da kan jama'a ta yadda za su fahimci cewa hukumar na da kyawawan tsare-tsaren ingantawa da bunƙasa fannonin watsa labarai. Ba ƙaƙaba takunkumi ko ladabtarwa kaɗai ne aikin hukumar ba.
"Ina sane da cewa ku na ƙoƙari sosai, amma akwai buƙatar ku ƙara ƙaimi a waɗannan batutuwa domin sai fa idan kun yi haka ne 'yan Nijeriya za su daina kallon cewa ba ku da wani tasiri sai hukunta kafafen da su ka karya doka kawai. Ku tashi ku nuna ku abokan haɗa hannu da ƙarfi ne domin kawo ci gaba."
Ministan ya ƙara da cewa ƙoƙarin da ake yi yanzu haka a Majalisar Tarayya don yi wa Dokar NBC garambawul abu ne mai kyau.
Ya ce, "Saboda lokacin da aka kafa NBC, ba a yi la'akari da wasu muhimman batutuwa ba, dalili kenan buƙatar yi wa dokar garambawul ta taso."
Idris, wanda shi ne Kaakaki Nupe, ya nuna gamsuwar sa ganin irin hoɓɓasan da NBC ta yi a shirye-shiryen ɗaukar nauyin taron AFRICAST da za a yi a cikin wannan wata.
Da ya ke bayani ga ministan, Babban Daraktan NBC, Malam Balarabe Shehu Ilelah, ya ce hukumar na da rassa 28 a cikin jihohi daban-daban, sai Ofisoshin Shiyya guda goma, sannan kuma ta na da ma'aikata 419.
Ya ce NBC ta na sa ido kan tashoshi 777, waɗanda a cikin su akwai gidajen rediyo 609 da tashoshin talbijin 168.
Ya ce, "Yayin da mu ke aikin sa-ido, mun bada gargaɗi sau 3,312 a 2022 da 2023. Cikin 2022 kuma an hukunta tashoshi 125.
"Mun aika da gargaɗi sau 1,238 a cikin 2023, sannan kuma an ladabtar da tashoshi 62."
Ilelah ya shaida wa ministan cewa NBC na bin gidajen rediyo da tashoshin talbijin bashin da ya haura naira biliyan uku.
Ya ce dalili kenan ma a cikin Mayu 2022, hukumar ta buga sunayen dukkan waɗanda ta ke bi basussukan a cikin jaridun ƙasar nan.
Ya ce, "Daga lokacin ne mu ka ba su wa'adin su canja lasisin su tare da biyan basussuka, ko kuma a soke lasisin baki ɗaya.
"An samu tashoshi 52 da ba su biya ba, watanni uku bayan cikar wa'adi. Hakan ne ya sa NBC ta yi amfani da doka, ta soke lasisin su a ranar 19 ga Agusta, 2022."
Hoto:
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a tsakiya), tare da Babbar Sakatare ta ma'aikatar, Dakta Ngozi Onwudiwe, da Babban Daraktan Hukumar Rediyo Da Talbijin ta Ƙasa (NBC), Alhaji Balarabe Shehu Illelah, a lokacin ziyarar