Matar da Mijinta ya gudu ya barta da 'Ya'ya 4 saboda halin Rayuwa...
- Katsina City News
- 19 Aug, 2023
- 951
Cikin Ikon Allah, Al'umma masu zuciyar taimakawa sun kawo ɗaukin gaggawa ga baiwar Allah, da Mijinta ya gudu ya barta da 'Ya'ya 4 Inda Yunwa ta kamasu ita kuma a wajen yawon neman taimako (Bara) aka banketa ta kare ƙafa.
A halin yanzu Ankaita Asibitin koyarwa ta Gwamnatin tarayya dake Katsina, domin kula da lafiyarta wanda majiyarmu ta tabbatar da cewa tsohon Dan takarar Majalisar Tarayya Hon. Sani Aliyu Danlami ya dauki nauyi. Su kuma yaran an garzaya dasu Asibitin kula da kananan yara da mata masu juna biyu domin tabbatar da ingancin lafiya, wanda likitoci suka tabbatar da basu da wata matsala da ta wuce yunwa.
Har yanzu suna bukatar cigaba da taimakawa, dafatan Allah ya bawa waɗanda suka bada gudunmawa lada Allah ya saka masu da Alkhairi.
Yanzu haka Matar tana samun kulawar Likitoci a yayin da aka maido 'Ya'yan gida, sabuwar Unguwar Shagari Lokas.