Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi - Sojin Nijar
- Katsina City News
- 19 Aug, 2023
- 821
Wannan ɗaya ne daga cikin jiragen yaƙi na Super Tucano da Mali ta saya a watan Yulin 2018Image caption: Wannan ɗaya ne daga cikin jiragen yaƙi na Super Tucano da Mali ta saya a watan Yulin 2018
Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi ɗai-ɗai don nuna goyon bayansu ga sojojin mulkin ƙasar da suka yi juyin mulki a watan Yuli.
Wani rahoto da kafar talabijin ɗin RTN ta gwamnatin ƙasar ta yaɗa ranar Juma'a ya ce ƙasashen biyu sun fara cika alƙawarin da suka ɗauka na taimaka wa Nijar kare kanta daga harin da Ecowas ke shirin kai mata don dawo da mulkin farar hula.
"Mali da Burkina Faso sun fara ɗaukar matakan cika alƙawari ta hanyar aiko da jirage don kare duk wani hari a kan Nijar," in ji rahoton.
An bayyana cewa jiragen na kai hari ne ƙirar Super Tucano.
A jiya Juma'a hafsoshin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato Ecowas suka ce sun saka ranar da za su afka wa Nijar don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Sai dai sun ce ba za su faɗi ranar ba, kuma za a ci gaba da yunƙurin shawo kan lamarin ta hanyar difilomasiyya.