Daga Ibrahim Badamasi Babangida, Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya
Muazu Hassan | Katsina Times
A ranar Asabar, 12 ga Yuni, 1993, an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa kamar yadda aka tsara. Abin mamaki a gare ni shi ne yadda zaɓen ya gudana cikin lumana sosai. An yi zaɓe a dukkan rumfunan zaɓe 110,000 da ke faɗin ƙasar nan, kuma bisa tsarin Modified Open Ballot System (MOBS) da Dokar Decree 13 ta tanada, an ƙidaya ƙuri’u a fili ba tare da wata matsala ba. Haka kuma, tattara sakamakon ya gudana a bayyane, wanda ya sa aka samu sakamakon ƙarshe cikin sauri.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (NEC) ta fara nuna sakamakon da aka samu daga hedkwatocin jihohi 30 a babban allo da ke ofishinta na Abuja tun daga ranar 13 ga Yuni, kamar yadda dokar zaɓe ta tanada. Wannan ci gaba ya kai jihohi 14 kafin ranar 14 ga Yuni.
Amma a ranar 16 ga Yuni, ba tare da sanina ko amincewata ba, shugaban NEC, Farfesa Humphrey Nwosu, ya sanar da dakatar da bayyana sakamakon zaɓen 12 ga Yuni har sai wani lokaci na gaba.
Nan take na fahimci cewa akwai wasu mutane a cikin gwamnati da ke ƙoƙarin kawo cikas ga tsarin, kuma akwai buƙatar taka-tsantsan.
Bayan dakatar da bayyana sakamakon, ƙungiyar Association for Better Nigeria (ABN) ta samu wata umarnin kotu daga Alƙali Saleh a Abuja wanda ya hana ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen.
Dakatar da sanar da sakamakon ya jefa ƙasar cikin rudani da rikici.
Ƙungiyoyi da dama kamar Campaign for Democracy (CD), ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, Nigerian Bar Association (NBA), Nigerian Medical Association (NMA), Women in Nigeria (WIN) da Association of Nigerian Authors (ANA) sun yi zanga-zanga da Allah wadai.
Da rikicin ya fara ƙamari, na koma gidana da ke Minna domin yin tunani tare da tattaunawa da mutane daban-daban daga cikin sojoji da fararen hula kan yadda za a magance matsalar, ba tare da sanin cewa wani abu mafi muni yana shirin faruwa ba.
A safiyar ranar 23 ga Yuni, na tashi daga Abuja zuwa Katsina domin yin ta’aziyyar rasuwar Alhaji Musa Yar’Adua.
Bayan an gama jana’izar, yayin da nake shirin komawa, sai na samu rahoton cewa an soke zaɓen 12 ga Yuni.
Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda aka yi sanarwar soke zaɓen. An kuma dakatar da dukkan shari’o’in da suka shafi zaɓen, an soke dokokin da suka shafi tsarin mika mulki, har ma da dakatar da NEC.
Sanarwar soke zaɓen ta fito ne ta bakin Nduka Irabor, sakataren yaɗa labarai na Admiral Augustus Aikhomu, daga wata takarda mara tambarin shugaban ƙasa ko ta gwamnati. Wannan ya girgiza ni matuƙa.
Hakika, an taɓa tattauna yiwuwar soke zaɓen a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin warware matsalar, amma ba a taɓa amincewa da hakan ba. Don haka ganin an yi irin wannan sanarwa ba tare da izinina ba ya ba ni mamaki ƙwarai. Na ce a raina: “Waɗannan mutane masu fuska biyu da ke cikin gida na sunyi aikin nasu”
Daga baya na gano cewa waɗannan mutane, ƙarƙashin jagorancin Janar Sani Abacha, su ne suka soke zaɓen. A lokacin ne na fahimci cewa na tsinci kaina cikin tsaka mai wuya.
Bayan soke zaɓen, ƙasar ta shiga ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen siyasa a tarihinta.
Campaign for Democracy ta shirya zaman gida wanda ya sa shaguna da kasuwanni suka rufe musamman a Legas da yankin Kudu maso Yamma.
Nigerian Labour Congress (NLC) da National Association of Nigerian Students (NANS) sun shiga zanga-zangar. A cikin shugabancin sojoji ma, mutane da dama sun nuna fushinsu. Janar Salihu Ibrahim, Manjo Janar Ishola Williams da Kanar Abubakar Dangiwa Umar sun nuna rashin amincewarsu. Har ma Dangiwa Umar ya yi barazanar yin murabus.
Jama’a sun ɗora mini laifin komai. Jaridu sun kira ni da sunaye iri-iri, suna zargina da son ci gaba da mulki.
A lokaci guda kuma an fara yaɗa jita-jita da ƙage don kare soke zaɓen. Wasu sun ce MKO Abiola ya shirya korar manyan hafsoshin soja idan ya hau mulki. Wasu kuma sun yi iƙirarin cewa gwamnati ta bari zaɓen ya gudana ne saboda tana tunanin Bashir Tofa zai yi nasara.
Waɗannan duka ƙarya ce. Duk da cewa a zuciyata wani lokaci na yi shakkar ko Abiola zai iya zama shugaban ƙasa mai tasiri, amma da yake an gudanar da zaɓen kuma ya bayyana a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓe mafi gaskiya a tarihin Najeriya, na yi imanin cewa dole ne a mutunta sakamakon.
Sai dai kuma akwai babbar matsala a cikin rundunar sojoji. Sojojin sun kasu gida biyu: masu goyon bayan mika mulki ga farar hula da kuma masu adawa da hakan, musamman idan Abiola ne zai zama shugaban ƙasa.
An kuma samu rahotannin makirce-makirce na kifar da gwamnatina ko kuma kashe ni. Daga baya na gano cewa wasu daga cikin manyan abokan aikina, ciki har da Janar Sani Abacha, suna cikin waɗanda ke shirya makirci a kaina.
Duk da haka, saboda tsoron barkewar fadan cikin gida, babu wanda ya yi yunƙurin aiwatar da waɗannan shirye-shirye.
Bayan tattaunawa da dama, na gana da MKO Abiola domin neman mafita. Na ba shi tayin shiga wata gwamnatin riƙon ƙwarya yayin da ake ƙoƙarin warware matsalar, amma ya ƙi amincewa. Ba wanda zai zarge shi, domin ya yi imanin cewa shi ne ya lashe zaɓen.
Daya daga cikin manyan matsalolina a lokacin shi ne Janar Sani Abacha. Mun daɗe muna abota, kuma ya taba ceton rayuwata tare da taimaka mini wajen karɓar mulki a 1985. Amma daga baya na gano cewa yana aiki a bayan fage yana yaɗa ra’ayoyin da ke nuna ni a matsayin matsala.
Na kuma gano irin ƙiyayyar da yake yi wa Abiola duk da cewa mutane suna tunanin suna da kyakkyawar alaƙa.
A ƙarshe, bayan tarurruka masu yawa, an yanke shawarar kafa Gwamnatin Riƙon Ƙwarya (ING) ƙarƙashin Ernest Shonekan. Domin tabbatar da dorewar gwamnati, an bar wasu manyan hafsoshin soja ciki har da Janar Sani Abacha a muƙamansu. A yau, mun san cewa wannan babban kuskure ne.
A ranar 27 ga Agusta, 1993, bayan na rattaba hannu kan Dokar Decree 61 da ta kafa ING, na sauka daga mulki bayan shekaru takwas a matsayin Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, sannan na koma gida Minna.
An ciro wannan daga littafin "A Journey in Service: An Autobiography" na Ibrahim Badamasi Babangida, wanda Bookcraft ta wallafa a shekarar 2025.