’Yansanda sun cafke mutum 344, sun ceto 27 daga hannun masu garkuwa a Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06052026_190359_FB_IMG_1778094164089.jpg



Auwal Isah Musa | Katsinatimes 

Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina ta ce ta samu gagarumar nasara a fannin tsaro a watan Afrilun nan da ya gabata na 2026, inda ta cafke mutum 344 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban, tare da ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ta rundunar ta kira ciki har da jaridun Katsina Timesna ranar Laraba.

Ya ce rundunar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ’Yansanda na jihar, CP Ali Umar Fage, ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da manyan laifuffuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, fadan daba, satar shanu da safarar makamai.

A cewarsa, sun samu waɗannan nasarori ne ta hanyar amfani da sahihan bayanan sirri, haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, da kuma ƙarfafa sintiri a wuraren da ake zargin aikata laifi.

DSP Aliyu ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka cafke akwai: Mutum 2 da ake zargi da garkuwa da mutane; Mutane 15 da ake zargi da fashi da makami; Mutane 8 da ake zargi da satar shanu da alaka da ’yanbindiga; Mutane 4 da ake zargi da bai wa ’yanbindiga bayanai; Mutune 28 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi; Mutane 28 da ake zargi da kisan kai; da Mutane 57 da ake zargi da zama ’yandaba.

Ya ƙara da cewa rundunar ta samu jimillar manyan laifuka 151 a watan, inda tuni sun riga da gurfanar da 128 daga cikinsu a gaban kotu bayan kammala bincike.

Rundunar ta ce ta kuma samu nasarar ceto mutane 27 daga hannun masu garkuwa da mutane, wadanda tuni an duba lafiyarsu tare da tantance su, kafin a mayar da su ga iyalansu cikin koshin lafiya.

Har ila yau, rundunar ta tabbatar da cewa ta kuma samu nasarar hallaka wani da ake zargi da garkuwa da mutane a yayin wata arangama da jami’anta suka yi da shi.

’Yansandan sun ce sun ƙwato kayayyaki da dama da ake zargin na aikata laifi ne, ciki har da: Kwamfutoci (laptops) guda 20; Wayoyin hannu guda 2; Makullin buɗe mota (master key) guda 1; Takardun shaidar dankasa NIN guda 62; da Na’urar ‘scanner’ guda 1

Sauran sun haɗa da: Dabbobi 243 da ake zargin na sata ne; Motoci guda 2 da aka sace; Babura guda 2; Kwayoyin Exol guda 48; Kwayoyin Tramadol guda 80; da kuma Sinki-sinkin wiwi guda 32. Rundunar ta ce dukkan kayayyakin suna hannunta kuma za ta gabatar da su a gaban kotu a matsayin hujja.

A cewar rundunar, ta kuma gudanar da samame da bincike na dare a wurare daban-daban domin dakile miyagun laifuka. Haka kuma ta ƙarfafa sintiri a manyan hanyoyi, musamman hanyar Funtua zuwa Zaria.

Rundunar ta yaba da haɗin gwiwar da take samu daga sauran hukumomin tsaro, inda ta ce hakan ya taimaka wajen saurin kai ɗauki da kuma nasarar ayyukanta. Hakazalika, ta ta gode wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar bisa goyon baya da haɗin kai da ake ba ta, tare da kira gare su da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka.

Follow Us