Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Katsina Times | 9 ga Afrilu, 2026
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, Academic Staff Union of Universities (ASUU), ta ƙaddamar da sabon ginin sakatariyarta na reshen Jami'ar Umaru Musa Yar'adua (UMYU) da ke jihar Katsina, tare da kira ga gwamnatocin tarayya da jihohi da su gaggauta aiwatar da yarjejeniyar 2025 da aka cimma da ƙungiyar.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Alhamis, 9 ga Afrilu 2026, inda manyan baƙi suka halarta ciki har da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Professor Salihu Muhammad, tare da malamai da ma’aikatan jami’ar.
Shugaban ASUU na ƙasa, Chris Piwuna, wanda Farfesa Lawal Abubakar ya wakilta, ya bayyana ginin a matsayin babban ci gaba da ke nuna haɗin kai da jajircewar mambobin reshen UMYU.
Ya ce mambobin ƙungiyar sun yi ƙoƙari matuƙa wajen ganin an kammala aikin duk da ƙalubalen da suka fuskanta, inda ya bayyana ginin a matsayin wata alama ta sadaukarwa da biyayya ga manufofin ASUU.
“Wannan gini ba kawai ofis ba ne, alama ce ta juriya da haɗin kai da kuma sadaukarwa ga ci gaban ƙungiyarmu,” in ji shi.
Ya kuma yabawa shugabancin reshen UMYU ƙarƙashin shugaban da ke shirin sauka, Dr. Murtala Abdullahi Kwara, da kuma shugabannin shiyyar Katsina bisa yadda suka gudanar da aikin cikin tsari da kwarewa har aka kammala shi cikin lokaci.
ASUU ta jaddada cewa dole ne gwamnati ta dinga kallon ƙungiyar a matsayin abokiyar hulɗa wajen gina ƙasa, ba abokiyar gaba ba, tana mai cewa jami’o’i na da muhimmiyar rawa wajen warware matsalolin ƙasa.
Ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su fara aiwatar da yarjejeniyar ASUU da gwamnati ta 2025 ba tare da ɓata lokaci ba, tana gargadin cewa haƙurin mambobinta na ƙasa yana ƙara ƙarewa.
Haka kuma, ƙungiyar ta buƙaci a sake duba ɓangaren walwalar ma’aikata na yarjejeniyar domin dacewa da halin tattalin arzikin da ake ciki yanzu.
“Inganta walwalar malamai ba alfarma ba ce, wajibi ne domin samar da ingantaccen ilimi, bincike mai amfani da kuma hidimar al’umma,” in ji sanarwar.
ASUU ta kuma buƙaci mambobinta da su ci gaba da jajircewa wajen fafutukar ganin an inganta ilimi a jami’o’in gwamnati domin makomar ɗalibai da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Ana sa ran sabuwar sakatariyar zata zama cibiyar gudanar da ayyukan ƙungiyar da kuma ƙarfafa fafutukar tabbatar da ingantaccen ilimi a jami’o’in Najeriya.