Katsina Times
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta bukaci Alhaji Jibrin Tanimu da ya gaggauta janye zargin da ya yi cewa hukumar ta sace masa Naira miliyan 221, tana mai cewa zargin “karya ne kuma bata suna.”
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 29 ga Maris, 2026, wadda Sakataren Hukumar kuma Mai Ba da Shawara kan Shari’a, Jabir Bello Esq, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce Tanimu ya yi wannan zargi ne bayan kama shi a ranar 10 ga Maris, 2026 a gidansa da ke Katsina.
Hukumar ta kara da cewa Tanimu ya kuma mika wannan zargi ga lauyoyinsa, wadanda suka rubuta wa Gwamnatin Jihar Katsina wasika suna zargin hukumar da sace kudin.
Sai dai hukumar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa “karya ne tsagwaronta, mara tushe kuma cike da mugunta,” tana zargin Tanimu da kokarin bata sunanta da kuma kawo rudini ga jama’a da hukumomin gwamnati.
Ta ce zargin ya jawo babbar illa ga martabar hukumar da jami’anta.
Dangane da yadda aka kama shi, hukumar ta ce ana zargin Tanimu da karbar Naira miliyan 10.2 ta hanyar yaudara daga wasu mutane uku, Aminu Ado Yakasai, Mas’udu Armaya’u Abbas da Aminu Garba Yakubu duk mazauna Jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa wani jami’in Hisbah ne ya hada wadannan mutane da Tanimu, inda daga bisani aka tsare jami’in a wata kotu a Kano, wadda ta umarci hukumar ta gabatar da Tanimu a gabanta a matsayin sharadin sakin jami’in.
Saboda haka, hukumar ta gabatar da bukatu guda hudu ga Tanimu, ciki har da ya janye zargin a rubuce, ya bayar da hakuri a fili ta hanyar wallafawa a kalla jaridu biyu na kasa, sannan ya daina yin irin wadannan kalamai na bata suna.
Hukumar ta kuma bukaci ya tabbatar a rubuce cikin kwanaki bakwai da karbar wasikar cewa ya bi wadannan umarni.
Ta yi gargadin cewa rashin bin wadannan bukatu zai tilasta mata daukar matakin shari’a, ciki har da neman diyyar bata suna da kuma umarnin kotu domin hana ci gaba da irin wadannan kalamai.
An kuma aika kwafin wasikar ga Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, Daraktan Hukumar DSS a jihar, da kuma Gwamnan Jihar Katsina.