ME YASA AKA CHANZA MA SHEMA MUKAMI?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20012026_222844_IMG-20260120-WA0247.jpg



Muazu Hassan  @ katsina times 

Facebook page: katsina city news.

A tsakiyar watan Mayu na shekarar 2025 ne,aka shelanta cewa shugaban kasa, ya ba  tsohon gwamnan katsina Barrister Ibrahim shema con mukamin shugaban hukumar gudanarwar cigaban Babban birnin tarayyar Abuja.
Jaridun yanar gizo sunyi ta yayata labarin.masoya sunyi taya shema murna. Watanni  tara da waccar sanarwar babu labarin yaushe Shema zai kama aiki sai kuma ga sanarwa ta biyu a cikin wannan watan na janairu 2026 cewa an chanza ma shema mukami zuwa shugaban hukumar " Shippers council of Nigeria "aka kuma bashi takarda da ofis  ranar 19 ga watan janairu 2026. Me ya kawo chanjin? 
Majiyoyi daban daban sun fada ma jaridun katsina times cewa .wasu gwamnoni da wasu mutane daga katsina sune suka yaki da a tabbatar wa da Shema wannan mukami.
Wani ya fada ma jaridun katsina Times cewa, an rubuta takardun korafi kala daban daban kuma a ofisoshi daban daban.
Abun da ya sa, aka yaki kujerar shine  saboda  muhimmacin ta da karfi da kuma hanyoyin samun kudi dake a cikin ta.
Majiyoyi suka ce korafi da kai zuga, ya sanya aka kasa  hada membobin hukumar ta raya birnin na Abuja.
Ganin lamarin yaki ci yaki cinyewa ya sanya shugaban kasa ya chanza ma Shema kujera daga "FCDA" zuwa "Shippers council " kuma aka bashi takarda tare da bashi ofis nan take.
Katsina Times ta tuntubi jami in kula da "social media "  na Shema akan me suka sani akan chanza wannan mukami? 
Mai Iyali ya fada mana cewa ,ita hukumar FCDA Ba ayi mata membobin ta ba.kuma ana ta samun jinkiri wajen sanar da membobin ta,wannan ya sanya shugaban kasa ya chanza ma Dakta Shema wata kujerar. Ya kara da cewa a sabuwar kujerar har ya shiga ofis.Muna masa addu a da fatan Alheri. 
Katsina Times 
Www.katsinatimes.com 
Facebook page: katsina city news 
Jaridar Taskar labarai 
All social media handles katsina times 
07043777779

Follow Us