Tun lokacin mulkin Sarakunan Habe na Katsina, Katsina itace babbar cibiyar Kasuwancin SAHARA ta Kasar Hausa. Mulkin Habe ya fara daga Sarkin Katsina Muhammadu Korau ( 1348-1398). Tarihi ya nuna cewa ta hanyar Kasuwancin SAHARA ( Transharan Trade) Addinin Musulunchi yazo Katsina. Hakanan kuma tun lokacin mulkin Habe, a sanadiyyar Kasuwancin SAHARA a Katsina an samu Kafuwar Unguwanni, wadanda yawancin su bakin Yan Kasuwane daga Kasashen Agades da North Africa, suka kafasu, daga cikin Kasashen da suka kafu a Katsina a wancan lokacin akwai Unguwar Albaba, wadda Berbers ne suka kafata daga Kasar Algeria, akwai Sararin Tsako wadda Buzayen Agades suka kafata, akwai Yansiliyu, Darma, da sauransu. Kasar Katsina ta kasance babbar cibiyar Kasuwancin SAHARA tun daga Habe, har zuwa shekarar 1807, lokacin da masu Jihadi suka kwaci mulki daga hannun Habe.
DALILIN KOMAWAR CIBIYAR KASUWANCIN KANO, DAGA KATSINA.
A lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio ne, acikin shekarar 1807, Mujahudai a karkashin Jagorancin Malam Ummarun Dallaje, da Malam Na Alhaji da Ummarun Dunyawa, da sauran mataimakansu, suka Kori Sarakunan Habe daga Katsina suka koma Maradi, da zama, a inda su Haben suka kafa Sarautar Sarkin Katsina Maradi, da hedikwatar su a Garin Maradi. Tun daga wannan lokacinne su Haben suka ci gaba da kawo ma Katsina hari da niyyar su kwaci mulkinsu daga hannun Fulani Dallazawa. Daga Kuma su Haben suka toshe hanyar da yawancin Fataken Yan Kasuwa Dake shigowa Katsina ta hanyar Maradi, da sauran Garuruwan Maradin. Wannan harin na Sarakunan Habe yasa yawancin bakin Yan Kasuwa masu hudda da Katsina suka koma huddata yarsu da Kano. Sannan Kuma wasu mazauna Katsina da suka hada da Yan Kasuwa da Malamai, suka yi hijira daga Katsina suka koma Kano, saboda yawan hare haren yakin da Sarakunan Habe suke kawo ma Katsina. Wannan dalilin yasa aka samu Unguwanni irin su Galadunchi, da Darma da sauransu a Kano, wanda wasu masana Tarihi sun nuna cewa mutanen Katsina da suka Kaura zuwa Kano a dalilin hare haren Sarakunan Habe suka kafasu.
Wannan shine babban daliln da yasa cibiyar Kasuwancin SAHARA ta tashi daga Katsina ta koma Kano. Wannan yasa a karshen Karni na 19 ( K19) Kano ta zama Mafi rinjayen Kasuwa a Afirika.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.