Daga wakilanmu Katsina Times
Wasu fulanin daji da ake zargin tubabbun "Bandits" ne, sun auka ma wani tubabben kwamandan barayon daji da ake kira da Mani kuma ake masa lakabi da Manin Tururuwa da tsakiyar rana a kasuwar Batsari a ranar alhamis 8/1/2026.
Lamarin ya faru a gaban wakilan Katsina Times, inda fulanin suka samu Manin Tururuwa a kara wajen sayar da dabbobi suka shiga sarar shi da adda da bugu da itace.
Wakilanmu da akayi lamarin gaban su wadand sun je kasuwar ne,don wani aikin sa ido ga zaman lafiya a yankin Batsari sun ce
Jama a na ganin fulanin sun fara bugun Mani Tururuwa sai kowa ya yi ta kansa ya nemi mafaka, wasu 'yan uwan Manin da sukayi, yunkurin kawo masa dauki nan suma maharan suka hada dasu.
Bayan da fulanin suka tabbatar da Mani ya fita hayyacinsa sai suka barshi cikin jini da halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Daga baya da kowa ya watse "yan sanda suka zo suka dau Mani Tururuwa zuwa asibitin Batsari.
Mani Tururuwa rikakken Bandits ne dan asalin Illela ta karamar hukumar Safana, jahar katsina. Ya amshi sulhu ne da barin sata da fashi lokacin Gwamnatin Masari.
Bayan tuban sa sai ya komo katsina da zama ya rika sana ar sayen dabbobi. Akwai kuma lokacin da aka ce ya sake daukar Makami yana yakar fulanin da basu yarda da sasanci ba.
Wani da yaso kawo ma Mani dauki don ya cece shi mai suna Saidu Dan tashshi shima ya sha bugu da sanduna, ance saidu yana auren 'yar uwar Mani.
Majiyoyi daban daban sunce harin da aka kaima Mani an kai masa ne saboda daukar fansa da tsohuwar gabar su ta tsaffin barayi.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page; katsina city news
Jaridar Taskar labarai @ Facebook page
Katsina Times on the social media handles
07043777779