UMYU Ta Fara Babban Shirin Sabunta Tsarinta, Ta na neman Jama'a Su Ba da Shawarwari

Daga WakilinmuJami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina ta fara wani babban shiri na sake fasalin martabarta da tsarinta, domin ƙara inganta matsayinta, ƙarfafa asalin cibiyar da manufofinta tare…

Katsina City News September 04, 2026  ·  12:00 AM
| 47 Views
UMYU Ta Fara Babban Shirin Sabunta Tsarinta, Ta  na  neman Jama'a Su Ba da Shawarwari
UMYU Ta Fara Babban Shirin Sabunta Tsarinta, Ta na neman Jama'a Su Ba da Shawarwari


Daga Wakilinmu

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina ta fara wani babban shiri na sake fasalin martabarta da tsarinta, domin ƙara inganta matsayinta, ƙarfafa asalin cibiyar da manufofinta tare da tsara alkiblarta bisa sabbin sauye-sauyen da ke faruwa a fannin ilimi mai zurfi.

Majalisar Gudanarwa da Hukumar Gudanarwar Jami’ar ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da Sakataren Kwamitin Sabunta Tsarin UMYU ya fitar.

A cewar sanarwar, shirin zai haɗa da bitar muhimman sassan da suka shafi asali da martabar Jami’ar, ciki har da manufofinta na aiki da hangen nesa, tambarinta, kalamanta na hukuma da kuma taken Jami’ar.

Jami’ar ta bayyana cewa wannan shiri wani muhimmin mataki ne na gina ingantaccen asali da martabar cibiyar, ƙara bayyana da jan hankalin jama'a zuwa gare ta, tare da daidaita ayyukanta da ƙa’idojin ilimi da bincike na ƙasa da na duniya.

A matsayin wani ɓangare na shirin, Jami’ar ta gayyaci al’umma, masu ruwa da tsaki da kuma membobin ƙungiyar Jami’ar da su gabatar da shawarwari masu ma’ana da ƙirƙira waɗanda za su taimaka wajen aiwatar da wannan sabon tsari.

Advertisement

NRS Gateway

Jami’ar ta buƙaci masu bayar da shawarwari da su gabatar da ra’ayoyinsu kan fannoni daban-daban da ake son a sake dubawa, musamman manufofin Jami’ar, hangen nesanta, tambarinta, kalamanta na hukuma da kuma taken Jami’ar.

Haka kuma, an ƙarfafa jama'a su gabatar da shawarwarin da za su nuna yanayin Jami’ar, muhimman ƙimominta, tarihinta da kuma burinta na gaba.

Ana iya tura shawarwari, ra’ayoyi da sauran gudummawa ta hanyoyin da ke ƙasa:

Imel: rebranding@umyu.edu.ng

Layin bada shawara na UMYU: +234 705 720 8670

Sanarwar ta samu sa hannun Sakataren Kwamitin Sabunta Tsarin UMYU.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 1?