Soke aikin hanyar Funtua zuwa Katsina: Wa ke kishin Katsina, waye maƙiyin su? Me ya kamata jama'a su yi?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28102025_103523_Screenshot_20251028-113505.jpg

Wa ke kishin Katsina, waye maƙiyin su? Me ya kamata jama'a su yi?

Daga Ahmad Abdullahi 

A jihar Katsina, hanyoyi biyu ne mafi muhimmaci da suka haɗa jihar da wasu jihohi da ƙananan  hukumomi.

Hanyar farko ita ce wadda ta taso daga Kano zuwa Katsina, ta haɗe har zuwa ƙasar Nijar. Hanya ta biyu ita ce wadda ta taso daga Funtua, Bakori, Ɗanja, Malumfashi, Ƙanƙara, Ɗanmusa, Safana, Dutsinma, Kurfi, Batagarawa, sai Katsina.

Hanyar Katsina zuwa Kano, yau sama da shekaru ashirin ana ta ƙoƙarin gyaran ta, abin ya ci tura.
Ibrahim Kabir Masari 

Hanyar ta biyu ta Funtua zuwa Katsina, ita ce wadda tattalin arziƙin noma da tasirin siyasa da yawan jama'a suka fito da yankin.

Wani bangaren hanyar wanda ya faro daga Funtua zuwa Mararrabar Ƙanƙara, ya kuma haɗe da hanyar zuwa Kano ta Dayi da Gwarzo, wanda ya haɗa Kano da jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Muhimmacin wannan hanya ya sanya wani ɗan Katsina mai kishi, kuma wanda yake da ƙarfin tattalin arziƙi da haɗin gwiwar kamfani mai ƙarfi da kayan aiki, ya nemi a ba shi aikin hanyar.

Kamar yadda muka ji, ya dau watanni yana nema da cika duk wata ƙa'ida da  ake so, tare da ma shiga yarjejeniyar a ba shi aikin ya fara, in ya kai wani matsayi na kammala wani sashe, sai  a fara ba shi kuɗin aikin.

Kamar yadda muka ji, bayan cika duk ƙa'idar ba kamfani kwangila, wanda gwamnatin tarayya ta shata, sai aka kai  aikin gaban Majalisar ƙoli ta ministocin ƙasar nan, wanda shugaban ƙasa ke jagoranta.
Ziyarar Ma'aikatan Hanyar ga Sarkin Katsina 

A majalisar ƙasa, an tattauna muhimmacin hanyar ga Najeriya da al'ummar Katsina da jihohin Arewa maso yamma, aka kuma tattauna cancantar kamfanin da ya nemi a ba shi aikin.

Bayan duk an tabbatar da cewa aikin na da muhimmanci, kuma kamfanin ya cancanta, sai aka ba shi aikin, aka kuma shelanta a ba da aikin.

Kamfanin ya ce, ko ba kuɗin zai cigaba da aiki don yana son ya kammala cikin watanni 24.

Kamfanin,  da yake na wani ɗan Katsina ne, ya ce sun tattara duk ƙarfinsu, sun tara a juhar Katsina. Kamfanin ya faro aikin daga wurare uku - daga Funtua zuwa Katsina, daga Mararrabar Katsina zuwa Katsina sai kuma daga Katsina zuwa Mararrabar Katsina.

Cikin kwanaki da fara aikin duk suka ruɗa hanyar. Jama'a suka yi ta fitowa suna murna.

 Jami'an kamfanin sun kai ziyara wajen Sarakunan Katsina da Daura, inda suka jaddada masu alwashi da alƙawarin gama aikin cikin wata 24 ko da babu kuɗin  gwamnatin Tarayya. 
Aikin hanyar daga Kankara zuwa Katsina 

Ana cikin haka, kawai sai akaji cewa an soke aikin, ba wani dalili. Jama'ar yankin suka yi zaman takaici, sannan suka jira me gwamnatin tarayya za ta ce?

Ministan ayyukan ya ce, wai rashin kuɗi ya sa aka soke aikin. Amma fa kamfanin ya ce zai yi aikin ko ba kuɗin gwamnatin tarayya, wato zai iya yi a kan bashi.

Ana cikin wannan jimami, sai aka zo wajen wani taron siyasa. Sai cikin masu magana a taron, wanda ake kira kabir Ibrahim Masari, wanda yake shi ne mai taimaka wa Shugaban ƙasa a kan harkokin siyasa ya ce sune suka sanya aka soke aikin, domin a ta bakinsa "An sanya ƙwarya ba a gurbinta ba."

Labari ya zo cewa, ana zargin  Alhaji Kabir Masari shi ya jagoranci zuwa wajen shugaban ƙasa a kan lallai a soke aikin nan saboda kamfanin da aka ba aikin na ɗan adawa ne, kuma mai neman takarar gwamnan Katsina a jam'iyyar PDP, wanda ake kira Yakubu Lado Ɗanmarke.

An ce Shugaban ƙasa ya nuna masu, ku ƙyale shi ya yi aikin, mu riƙe shi yadda ba wani barazana da zai iya yi mana. Suka ce a'a, a dai soke. 

An ce Shugaban ƙasa ya nuna masu cewa, a aikin ci gaba ana ajiye siyasa, a kalli al'umma, amma suka dage kan cewa a soke kwangilar.

An soke kwangilar tun watan Yuli na shekarar 2024. Har yanzu ba dawo kan aiki ba. Kuma ba a ba wani kamfani ba, wanda wannan yana da wahalar gaske a sake dawowa kan batun gina hanyar.

A nan su waye maƙiyan ci gaban Katsina kenan? Jama'a sun fara magana, kuma sun fara tattaunawa a kan al'amarin. Hazo ya ɗauki zafi a kan me ya sa aka yi mana haka?

Kusan duk hanyoyin da aka bayar tare da wannan hanyar, ko dai an kammala su, ko ana gab da idarwa. Amma na hanyar Katsina an bar ta tana shan ƙura.

Mutane sun fi son a ba kamfanin da ya fara aikin, ya ci gaba domin na gida ne. Ko don jin kunyar siyasa da kishin al'ummarsa, dole ya yi aikin. Suna ba da misalin cewa aikin Kano zuwa Katsina ya fi shekaru ana ta sabatta-juyar ta, saboda baƙi ne suke aikin, wanda kuɗin da za su samu shi ne a gaban su.

Wasu na kusa da Gwamnan Katsina sun barranta Dikko Umar Radda da soke aikin hanyar. Sun ce aƙidar siyasar sa ta cigaba ce  da gina ƙasa.

Me ya kamata jama'a su yi? Lokaci ya yi da za su fito su yi magana a kan hanyar nan. Kuma ya kamata a faɗi   da babbar murya cewa, kamfanin da ya yi wahalar tabbatar da an ba shi aikin, a mayar masa domin na ɗan ƙasa ne kuma ɗan jiha.

Kuma arziƙin da zai samu, ƙasa da jihar ce za ta ƙaru, ba kamar wasu ba da kwashewa za su yi zuwa ƙasashen waje.

Mun ji labarin wasu kamfanoni sun nemi aikin, amma kuɗin da suka sanya ya nunka na kamfanin da ya fara aikin sau bakwai.

Ya kamata shugaban ƙasa da Gwamnan Katsina, su kuma sani a rantsuwarsu na kama aiki, sun ce ba ruwansu da jam'iyya, yare, ko wani yanki, al'ummar ƙasar ke a gabansu.

Lokaci ya yi da jama'a za su yi nazari a kan wannan aikin. Waye mai ƙaunar su, waye bai son cigaban su?

Follow Us