Tarihin Makabartar Sarakunan Musulunci Ta Dallazawa Da Makarantar Sarakunan Musulunci Ta Sullubawa Zuri'ar Sarki Muhammadu Dikko
- Katsina City News
- 13 Dec, 2024
- 75
MAKABARTAR SARAKUNAN MUSULUNCHI TA DALLAZAWA.
Dallazawa kamar yadda sunan su ya nuna sune zuruar Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje. Dallazawa sun amshi ragamar mulkin Katsina acikin shekarar 1806, bayan cin nasarar Jihadin Jaddada addinin musulunchi na Karni na sha tara ( K19). Dallazawa sunyi Sarakuna kamar guda takwas (8) a Katsina, wadanda suka hada da.
1. Ummarun Dallaje (1806-1835).
2. Saddiqu (1835-1844)
3. Muhammadu Bello (1844-1869)
4. Ahmadu Rufai(1869-1870)
5. Ibrahim (1870-1882)
6. Musa (1882-1887)
7. Abubakar (1887-1905)
8. Yero ( 1905-1906)
Wadannan sune jerin Sarakunan da suka yi Sarkin Katsina daga Zuruar Fulani Dallazawa.
Amma ga Tarihin Makabartar Sarakunan Musulunchi na Dallazawa ya nuna Sarakunan Dallazawa guda ukku(3) ne kadai aka rufe a Makabartar, sai Kuma Kabarin Galadima Dudi, Wanda yayi Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi daga shekarar 1808 zuwa 1821.
Ita wannan Makabarta ta Dallazawa tarihi ya nuna Mutum na farko da aka Fara rufewa a wannan Makabartar shine Galadiman Katsina Dudi, Wanda ya rasu acikin shekarar 1821, shi Galadima Dudi babban amine ne na Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje, lokacin daya ya rasu, sai Sarkin Katsina Ummarun Dallaje yace a kawo shi a rufeshu cikin Gidan Sarki kusa dashi, haka Kuma akayi acikin shekarar 1821. Bayan Galadima Dudi, Mutum na biyu da aka rufe Shine Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje Wanda ya rasu acikin shekarar 1835, shima anan cikin Gidan Korau aka rufeshi, wannan kuwa al'ada ce ta Sarakunan da, da Malamai idan sun rasu yawanci a Gidajensu ake rufesu. Daga Ummarun Dallaje sai Sarkin Katsina Ahmadu Rufa'i ( Garnakaki) Wanda ya rasu acikin shekarar 1870. Bayan shi sai Kuma Sarkin Katsina Malam Musa wanda ya rasu acikin shekarar 1887. Wadannan sune Sarakunan da aka rufe a Makabartar Sarakunan Musulunchi ta Dallazawa. To Amma a halin yanzu wannan Makabartar tana a Unguwar Tsamkya bayan Gidan Sarkin Katsina, ance a lokacin Mulkin Turawa, anyi gyara a Gidan Korau, a lokacin da Katangar ta Fadi, to sai aka fido Kaburburan suka dawo bayan Gidan Sarki.
Wani zaice Dallazawa suna da Sarakuna Takwas(8) a Katsina, to miyyasa Sarakuna Ukku(3) kadai aka rufe a Makabartar su ta Tsamiya?
Shi Sarkin Katsina Saddiqu Wanda aka nada bayan rasuwar Ummarun Dallaje acikin shekarar 1835, Tarihi ya nuna, Sarkin Musulmi ya tube daga Sokoto akan wasu matsali da suka faru acikin shekarar 1844, sai aka tafi dashi Sokoto, acan Sokoton ne ya rasu Kuma acan aka rufeshi. Bayan an Tube Saddiqu, sai.aka nada danuwansa ko Kuma ace yayan shi watau Sarkin Katsina Muhammadu Bello ( 1844-1869). Shima Muhammadu Bellon baa Gidan Korau aka rufeshi, ance Yana da Gonaki da Gandu a Nasarawar Rafukka, kamin ya rasu sai ya bar wasiyya cewa a rufeshi a Lambun shi dake Rafukka, haka Kuma akayi acikin shekarar 1869, yanzu haka Kabarin shi na can acikin Lambun.
Shi Kuma Sarkin Katsina Abubakar (1887-1905) Turawan mulkin Mallaka ne suka tube shi daga Sarauta acikin shekarar 1905, inda daga karshe suka kaishi Kano a matsayin dan Gudun Hijira. Sarki Abubakar ya rasu a Kano acikin shekarar 1940.
Shi ma Sarkin Katsina Yero (1905-1906) Turawan Mulkin Mallaka suka tube shi daga Sarauta sai suka tafi dashi Lokoja. Yero a Lokoja ya rasu, Kuma aka rufeshi acan acikin shekarar 1919.
MAKABARTAR SARAKUNAN MUSULUNCHI TA SULLUBAWA ZURUAR SARKIN KATSINA MUHAMMADU DIKKO.
Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944) shine Wanda ya kafa Daular Sullubawa ta Gidan Dikko, acikin shekarar 1906, a lokacin days hau kan gadon Sarautar Katsina. An haifeshi a shekarar 1865, a zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Bello. Ya zama Sarki Yana da shekara 41 da haihuwa. Yana d rike da Sarautar Durbi likkafarsa ta yi gaba, ya zama Sarkin Katsina. Daular Dikko ko Kuma Sullubawa, a halin yanzu sunyi Sarakuna guda hudu (4) a Katsina kamar haka:.
1. Muhammadu Dikko (1906-1944)
2. Usman Nagogo(1944-1981).
3. Muhammadu Kabir ( 1981-2008)
4. Abdulmumini Kabir (2008) zuwa yanzu. Har ya zuwa yanzu Sullubawa zuruar Gidan Dikko sune suke mulkin Katsina.
Makabartar Sarakunan Musulunchi ta Sullubawa, Daular Dikko tana nan a Tafkin Lambu, dake cikin Kofar soro. Asalin Makabartar Lambu ne na Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko, to sai shi Sarki Dikkon ta shifka wani Dabino a cikin Lambu yace idan ya rasu akawo a rufeshi kusa da Dabinon, haka Kuma akayi acikin shekarar 1944, bayan ya rasu sai aka kawo adai dai wannan Dabinon cikin Lambun shi aka rufeshi. Wannan ya nuna Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shine Sarki na farko da aka Fara rufewa a cikin Makabartar Tafkin Lambu ta Sullubawa. Daga shi Kuma sai Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo Wanda aka rufe a Makabartar acikin shekarar 1981. Bayan Sir Usman Nagogo sai Kuma Sarkin Katsina Muhammadu Kabir Wanda aka rufeshi acikin shekarar 2008. Wadannan sune Sarakunan da aka rufe a Makabartar Sarakunan Musulunchi ta Sullubawa. Yawanci Sarakuna ake rufewa a Makabartar da Matansu, amma baa rufe yayan Sarki ko Kannen shi.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.